Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da Kashe naira miliyan dubu 95 domin gyara madatsun ruwa guda 16 a Kano domin bunkasa noman rani da kuma kara aikin hanyar ring road da akafi sani da Eastern Bypass.
A wata sanarwa da sabon daraktan kudi na hukumar kula raya kogin Hadejia Hon Musa Iliyasu Kwankwaso ya fitar, ya bayyana cewa tuni aka kaddamar da kwamitin kwarraru da zai duba madatsun ruwan na jihar kano dake bukatar wannan aiki.
Kwankwaso yace kaddamar da kwamitin kwararru na tantance madatsun ruwan na Kano zai bibiyi madatsun ruwan Challawa Goge da Tiga da Wasai da na Karaye da sauransu .
Kwankwaso ya tabbatar wa da shugaba Tinubu cewa nadin da aka yi masa a matsayin Darakta ya karawa ‘yan jihar Kano kwarin guiwa wajen ganin an samar da hanyoyin tabbatar da manufar Shugaban kasa wanda yace hakan kamar sharar hanyar dawowar Tinubu mulki ne a shekarar 2027.

