Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da kashe kudaden da suka kai Naira miliyan 164 domin sake aikin gyaran babban Asibitin yara na Asiya Bayero da ke cikin birnin Kano.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ne ya bayyana hakan bayan kammala zaman majalisar zartaswa na jihar Kano karo na 33 a yayinda yake karin haske ga manema labarai na fadar gwamnatin Kano.
Ya ce, an amince da kudin ne a zaman majalisar zartaswa kuma an warewa bangaren lafiya kuɗi sama da naira miliyan 270 domin gyaran wasu manyan asibitoci ciki harda Asibitin Tiga.
Sannan kwamishinan na yaɗa labarai yace za’a, sabunta kayan aikin jinya, da kuma samar da sabbin dakunan kwana da ofisoshi domin inganta yanayin aiki da karɓar marasa lafiya.
TST Hausa ta rawaito cewa,zaman majalisar zartaswa karo na 33 ya amince a kashe kuɗade sama da naira miliyan dubu 19 domin yin wasu mahimman ayyukan raya kasa da bunkasa bangaren lafiya da Ilimi da samar da ruwan sha da sauransu.
A cewar kwamishinan, matakin ya kasance cikin shirin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na farfaɗo da cibiyoyin kiwon lafiya a fadin jihar, tare da nufin tabbatar da cewa kowane yanki yana da asibitin da ke ba da kulawa ta zamani.
Kwamared Wayya yace zaman majalisar ya kuma amince da gina gidaje guda 50 a kowacce karamar hukuma ta wajen birnin Kano domin bunkasa yankunan karkara.

