Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kira ga gwamnatoci a fadin duniya da su kara haraji kan abubuwan sha masu dauke da sikari da kuma barasa, tana mai gargadin cewa saukin samunsu da arha da suke da shi na haddasa babbar barazana ga lafiyar jama’a.
A cewar WHO, shan lemun kwalba mai dauke da sikari da barasa na taimakawa wajen yaduwar kiba,da ciwon suga,da cutar daji, da kuma raunuka da ke da alaka da shan barasa, lamarin da ke kara dora nauyi kan tsarin kiwon lafiya.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/who-ta-tabbatar-da-billar-sabuwar-cutar-coronavirus-a-china/
Daraktan Janar na WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai ta kafar yanar gizo.
Ya ce an riga an tabbatar da cewa kara harajin akan irin wadanan kayayyakin na rage yawan amfani da su da ke da illa ga lafiyar dan Adam.
Ya kara da cewa, baya ga kare lafiyar al’umma, irin wadannan haraji na samar wa gwamnatoci kudaden shiga da za a iya amfani da su wajen inganta kiwon lafiya,da ilimi da shirye-shiryen jin dadin jama’a.
Rahoton WHO kan harajin abubuwan sha masu sikari ya nuna cewa akalla kasashe 116 ne ke kakaba haraji kan irin wadannan abubuwan sha.
Sai dai rahoton ya ce har yanzu wasu kayayyaki masu dauke da sikari mai yawa na tsallake wannan haraji, ciki har da ruwan ‘ya’yan itatuwa kashi 100 cikin 100, madarar da aka kara mata sikari, da shaye-shayen kofi da shayi da ake sha kai tsaye.
A wani rahoto dabam kan barasa, WHO ta ce kasashe 167 ne ke kakaba haraji kan giya, da ruwan inabi da sauran barasa.
WHO ta jaddada cewa kara haraji kan kayayyakin da ke cutar da lafiya na daga cikin matakai mafi tasiri da gwamnatoci za su dauka wajen rage shan su,da kare lafiyar jama’a, da kuma rage mace-macen da za a iya kaucewa.

