Ɗan takarar gwamna a jihar Yobe a APC Barrista Kashim Musa Tumsah (KMT), da magoya bayansa sun sake tabbatar da goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, domin sake zaɓensu a babban zaɓen 2027.
Ya bayyana hakan ne bayan wani babban taro na KMT Movement, wanda ya haɗa wakilai da shugabannin ƙungiyoyin da ke goyon bayan Kashim Musa Tumsah daga sassa daban-daban na Jihar Yobe.
An gudanar da taron a Kaduna ranar Asabar, 3 ga Oktoba, 2026.
A yayin taron, mahalarta sun yi nazari kan halin da siyasar ƙasa da ta Jihar Yobe take ciki, tare da tattauna matakan da ƙungiyar za ta ɗauka yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
A cikin sanarwar da aka fitar bayan taron, KMT Movement ta ce ci gaba da kasancewa cikin APC da kuma yin aiki domin ganin an sake zaɓen Tinubu da Shettima na daga cikin muhimman abubuwan da suka sanya a gaba.
Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da kasancewa cikin Jam’iyyar APC, yayin da za ta buɗe ƙofa domin duba sauran hanyoyin haɗin gwiwa da damar siyasa da za su dace da muradun ƙungiyar da na Jihar Yobe.
Sai dai, dangane da zaɓen gwamnan Jihar Yobe na 2027, ƙungiyar ta ce har yanzu tana ci gaba da tuntubar mambobi da magoya bayanta kafin ɗaukar matsayar ƙarshe.
Yace Tinubu ne mafita ga Najeriya Amma Jama’a ba za su gane ba sai nan gaba.
Saboda haka, an umurci shugabannin ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin KMT Movement a sassa daban-daban na jihar da su koma yankunansu domin tattaunawa da mambobi da magoya baya, sannan su gabatar da rahotonsu ga sakatariyar ƙungiyar cikin kwanaki bakwai.
Haka kuma, KMT Movement ta ce za ta jira sakamakon ƙararrakin kotun da ke ƙalubalantar zaɓen fidda gwani na APC na takarar gwamnan Jihar Yobe da aka gudanar a watan Mayun 2026, kafin ta yanke matsayar ƙarshe kan matakin da za ta ɗauka a zaɓen gwamnan jihar.
Ƙungiyar ta jaddada cewa muradun Jihar Yobe, magoya bayanta da al’ummar jihar za su kasance cikin muhimman abubuwan da za su yi la’akari da su wajen yanke shawarar siyasa ta gaba.
A ƙarshen taron, an buƙaci shugabannin ƙungiyoyin KMT da su koma ga mambobinsu domin sanar da su matsayar da aka cimma, tare da ci gaba da tuntuba kan makomar siyasar Jihar Yobe.

