Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da aiwatar da sabon tsarin albashi ga ma’aikatan da ba malamai ba da kuma wadanda ke koyarwa a jami’o’in jihar guda biyu.
Jami’o’in su ne Jami’ar Aliko Dangote ta Kimiyya da Fasaha da ke Wudil da kuma Jami’ar Northwest da ke Kano.
Sabon tsarin albashin ya yi daidai da tsarin biyan albashin da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi tare da fara aiwatarwa a jami’o’in tarayya.
Mai magana da yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
A cewar sanarwar, amincewar ta biyo bayan rahoto da shawarwarin wani kwamiti da Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta kafa domin nazarin bukatar jami’o’in biyu na amfani da sabon tsarin albashin.
Sabon tsarin ya fara aiki ne daga Janairu 2026, yayin da za a fara biyan sabon albashin daga Satumba 2026.
Jimillar kuɗin da sabon tsarin zai ci gwamnati a kowane wata a jami’o’in biyu ya kai Naira miliyan 391.85, wanda ya yi daidai da kusan Naira biliyan 4.7 a shekara.
A Jami’ar Aliko Dangote da ke Wudil, sabon tsarin zai ci kusan Naira miliyan 228.2 a wata.
Yayin da na Jami’ar Northwest da ke Kano zai kai kusan Naira miliyan 163.65 a wata.
Gwamnatin jihar ta kuma amince da ware Naira biliyan 1.57 a cikin kasafin kuɗin kari na shekarar 2026 domin biyan sabon tsarin daga Satumba zuwa Disamba.
Haka kuma, za a tanadi Naira biliyan 3.13 a kasafin kuɗin shekarar 2027 domin biyan bashin albashin da ya taru daga Janairu zuwa Agusta 2026.
Gwamnatin ta ce matakin na da nufin inganta walwalar ma’aikatan jami’o’in, tabbatar da zaman lafiyar masana’antu da kuma ƙarfafa harkar ilimi mai zurfi a Jihar Kano.
Baya ga batun albashi, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma amince da duba yiwuwar kafa Kwamitocin Ziyara (Visitation Panels) a jami’o’in biyu da sauran manyan makarantun jihar.
An ce kwamitocin za su taimaka wajen ƙara riƙon amana, gaskiya da ingantaccen shugabanci, tare da tabbatar da gudanar da cibiyoyin ilimi yadda ya kamata.
Gwamna Yusuf ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta rayuwar ma’aikata da kuma zuba jari a harkar ilimi, musamman wajen bunƙasa ƙwarewar ɗalibai da samar da ingantaccen ilimi a Jihar Kano.

