Shugaban Babban Asibitin Hadejia da ke Jihar Jigawa, Dr. Habib Abubakar, ya yi kira ga likitocin Najeriya da su daina ƙaura zuwa ƙasashen waje domin gudanar da ayyukansu, yana mai jaddada cewa ƙasar na matuƙar buƙatar ƙwarewarsu wajen inganta harkokin lafiya.
Dr. Habib ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Hadejia.
Ya ce abin takaici ne yadda adadi mai yawa na likitocin Najeriya ke barin ƙasar domin neman ingantacciyar rayuwa da yanayin aiki a ƙasashen waje, lamarin da ke ci gaba da haifar da ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan lafiya a cikin ƙasar.
Sai dai ya bayyana cewa shi ba ya da niyyar barin Najeriya, kasancewar Gwamnatin Jihar Jigawa ta ba shi cikakken tallafi tun daga lokacin karatunsa har ya zama ƙwararren likita.
“Idan gwamnati ta ɗauki nauyin karatunka, ta ba ka duk wani tallafi har ka zama likita, bai kamata ka juya wa ƙasarka baya ba.
Najeriya na buƙatar hidimarka fiye da kowane lokaci,” in ji Dr. Habib.
Ya ƙara da cewa ci gaban da ake samu a fannin lafiya a Jigawa ya samo asali ne daga jajircewar gwamnatin jihar wajen inganta kayan aiki, horar da ma’aikata da kuma samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya.
Dr. Habib ya yabawa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa irin ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen bunƙasa harkokin lafiya, yana mai cewa matakan da ake ɗauka sun sanya har al’ummomin wasu jihohi ke amfana da ayyukan kiwon lafiyar da ake samarwa a Jigawa.
A ƙarshe, ya yi kira ga likitoci da sauran ma’aikatan lafiya da su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin gaskiya, riƙon amana da tausayi, tare da fifita rayuwar marasa lafiya da hidimtawa ƙasa a kan duk wani buri na ƙashin kai.

