Malam Usman Mai Dubun Isa ya burge jama’a a yayin gudanar da bukukuwan Takutaha a birnin Kano, bayan da ya tsayar da tawagarsa domin gudanar da Sallar Azahar a lokacin da ake ci gaba da tattakin Takutaha.
TST Hausa ta rawaito cewa an baiwa jagororin masu zagayen lokuta daban daban domin yin zagayen nasu domin kaucewa duk wani rikici ko tashin hamkali.
Lamarin ya ja hankalin jama’a sosai, musamman ganin yadda Mai Dubun Isa ya dage wajen ba da muhimmanci ga ibada tare da tabbatar da cewa ba a bari shagalin da ake gudanarwa ya hana tawagarsa tsayar da Sallah a kan lokaci.
A yayin da ake ci gaba da tattakin, an ga dandazon dubban jama’a sanye da fararen kaya, suna biye da tawagar Mai Dubun Isa a cikin yanayi na cunkoson jama’a da nuna kauna da girmamawa ga manzon Allah Annabi Muhammadu SAW.
Tsayar da tawagar domin Sallar Azahar ya zama abin lura ga mahalarta taron, inda jama’a suka nuna sha’awarsu kan yadda aka dakatar da tattakin domin gudanar da ibadar.
Bukukuwan Takutaha dai na daga cikin manyan abubuwan da ke jan hankalin jama’a a Kano, inda dubban mabiya da masu sha’awar al’adun addini ke taruwa domin gudanar da shagulgulan.
Hotunan taron sun nuna yadda dandazon jama’a sanye da fararen kaya ya mamaye titunan Kano, lamarin da ya kara nuna girman taron da yadda yake jan hankalin al’umma.

