Kwamishinan Matasa da Bunƙasa Wasanni na Jihar Borno, Sainna Buba, ya janyo ce-ce-ku-ce bayan da ya yi kalaman barazana ga masu adawa da jam’iyyar APC, inda ya ce za a mayar wa duk wanda ya nuna adawa da su martani mai tsauri.
Kwamishinan ya yi wannan furuci ne a wani taron ƙaddamar da yaƙin neman goyon baya da ƙungiyar Tinubu City Boy Movement ta shirya domin nuna goyon baya ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kuma yiwuwar sake tsayawarsa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
A yayin da yake jawabi ga mahalarta taron, Sainna Buba ya yi gargadin cewa ba za su lamunci adawar siyasa ba, inda ya yi amfani da kalaman da ke ɗauke da barazanar tashin hankali.
Ya ce duk wanda ya nuna musu yatsa, za su mayar masa da martani, har ma ya yi amfani da kalaman cewa za su “yanke” ko kuma “karya” yatsan wanda ya sake nuna musu adawa.
Kwamishinan ya kuma yi magana kan rabon alfarmar gwamnati, inda ya ce mutanen da ke tare da su za su ci moriyar gwamnati, yayin da waɗanda suka ƙi goyon bayansu za su fuskanci hukunci.
Kalaman na Sainna Buba sun jawo suka daga wasu masu ruwa da tsaki, waɗanda suka bayyana damuwa kan yadda irin wannan furuci daga jami’in gwamnati zai iya shafar tsarin dimokuraɗiyya da kuma ‘yancin ‘yan ƙasa na bayyana ra’ayinsu na siyasa.
Masu sukar lamarin sun ce ya kamata jami’an gwamnati su riƙa amfani da kalaman da za su ƙarfafa zaman lafiya da haƙurin siyasa, musamman yayin da ƙasar ke ƙara kusantar zaɓen 2027.
Ya zuwa lokacin da ake wannan rahoto, Sainna Buba bai yi wani ƙarin bayani kan kalamansa ba, kuma gwamnatin Jihar Borno ba ta fitar da sanarwar hukuma kan lamarin ba.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyar bayan Shugaban Karamar Hukumar Kuje a Babban Birnin Tarayya, Danjuma Shekwolo, ya buƙaci mazauna yankin da su zaɓi APC a zaɓen 2027 ko kuma su bar yankin.

