Wani jigon jam’iyyar APC daga Kano, Hon. Shehu Isah Direba , ya yi ikirarin cewa jam’iyyar ADC ba ta da isasshen karfin siyasa a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya kamar yadda ake kokarin nunawa.
Shehu Isah ya ce ya kamata tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ke cikin manyan jagororin tafiyar ADC, ya yi nazari kan hakikanin tasirin jam’iyyar a yankin, musamman idan aka yi la’akari da sakamakon zabukan baya.
Ya na wannan magana ne bayan sanar da sakamkon zaben gwamnan jihar Osun, inda ADC ta samu kuri’u dubu 17.
A cewar sa, kasancewar wasu fitattun ‘yan siyasa daga Kudu maso Yamma sun shiga ADC ko kuma suna rike da manyan mukamai a jam’iyyar, ba ya nufin cewa jam’iyyar ta samu karfin kuri’a a yankin.
Ya yi nuni da tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, wanda yanzu yake cikin manyan jiga-jigan ADC, yana mai cewa sakamakon zabe ne ya kamata ya zama ma’aunin auna karfin dan siyasa da jam’iyya, ba wai mukami ko yawan magoya baya a tarukan siyasa kadai ba.
Shehu Isah ya ce: “Babu ADC mai karfi a Kudu maso Yamma.
Atiku ya kamata ya san wannan. Idan babban jigon jam’iyyar kamar Aregbesola bai samu gagarumar kuri’a a yankinsa ba, to ya kamata a tambayi inda karfin ADC yake a yankin.”
Ya kara da cewa siyasar Najeriya ta bambanta da tarukan siyasa, domin abin da ke tabbatar da karfin jam’iyya shi ne yadda take iya juya goyon bayan jama’a zuwa kuri’u a ranar zabe.
Jigon APC din ya ce bai kamata shugabannin ADC su dogara da sunayen manyan ‘yan siyasa kawai wajen hasashen nasarar jam’iyyar a 2027 ba, sai sun tabbatar da cewa suna da ingantaccen tsari da karfin magoya baya a matakin mazabu da kananan hukumomi.
Ya kuma shawarci Atiku da sauran shugabannin ADC da su duba yadda jam’iyyar za ta gina tubalin karfi a yankin Kudu maso Yamma, maimakon dogaro da tasirin wasu ‘yan siyasa da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar.
Shehu Isah ya bayyana cewa kalubalen da ADC ke fuskanta shi ne mayar da farin jinin shugabanninta zuwa ainihin kuri’u, musamman a jihohin Kudu maso Yamma da ake ganin za su taka muhimmiyar rawa a babban zaben 2027.
Ya ce sakamakon zabuka ne zai bayyana ainihin karfin kowace jam’iyya, don haka ya kamata ADC ta yi amfani da lokaci kafin 2027 wajen karfafa tsarin jam’iyyar daga tushe.

