Close Menu
  • Shafin Farko
  • Labarai
  • Ketare
  • Siyasa
  • Noma da Kiwo
  • Yanayi
  • Tsaro
  • Karin Wasu
    • Kasuwanci
    • Ilimi
    • Nishadi
    • Muhalli
    • Lafiya
    • Ra’ayi
    • Wasanni
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp Telegram
TST HAUSATST HAUSA
  • Shafin Farko
  • Labarai

    Rikicin NDC: ’Yan Takarar Kano 5 Sun Kai Ƙara INEC, Sun Zargi Shugabannin Jam’iyya Da Hana Su Takara

    October 26, 2026

    SDP ta yi gargadi da kada a fake da Cutar Ebola a dage zaben 2027

    October 26, 2026

    Sai Shekarar 2031 Za Mu Bar Villa – Remi Tinubu

    October 24, 2026

    Duk Sakon Annabawa ya Tafi Ne kan A Bautawa Allah shi Kadai, In Ji Dr. Gadon Kaya

    October 23, 2026

    Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Da Gwamnatin Tinubu Ta Shigar Kan Samar Da Sabuwar Hukumar Bogi

    October 12, 2026
  • Ketare

    Yau Ake Toshe Shafukan Sada Zumunta na Yara yan Kasa da Shekara 16 a Australia

    December 4, 2025

    Rikicin Gaza:Sarkin Saudiyya ya amincewa Falasdinawa 1000 su shiga kasar su sauke farali kyauta

    May 19, 2025

    Duk wanda ya yarda zai bar Amurika ya koma kasarsa zamu bashi kyautar Dala 1000 – Inji Trump

    May 6, 2025

    Ba a ga jinjirin watan Shawwal a Saudiyya ba

    March 29, 2025

    An ga watan Sallah karama a Saudiyya

    March 29, 2025
  • Siyasa

    Dan Majalisar Minjibir Ne Ya Shigar Da Korafi Majalisar Akan Kama Kunnen Zomo

    October 19, 2026

    Ya Nemi Magoya Bayansa Da Kasa Su Yi Bakin Ciki

    October 19, 2026

    Kwankwaso ne ya fito da Sabo Bakin Zuwo a siyasar Kano — Aminu La Boys

    October 16, 2026

    Dan takarar ya ce Yobe ta Tinubu kuma shi za ayi a 2027

    October 5, 2026

    Gwani Dr. Waiya ya nemi Limaman su fadakar da Jama’a illar bangar siyasa

    October 5, 2026
  • Noma da Kiwo

    Za’a samu ƙarancin shinkafar Basmati da Indiya ke nomawa a bana

    September 4, 2025

    Tsadar rayuwa: Komai matsayin mutum a Najeriya ya koma gona,saboda abinda na hango -Inji wani Lauya

    December 15, 2024
  • Yanayi
  • Tsaro

    Yan sandan Bauchi ne suka gurfanar da su

    October 17, 2026

    Yan Bindiga Sunyi garkuwa da ’yan uwan Mataimakin Gwamnan Sokoto

    May 1, 2026

    An Kama Budurwa da Kunkuru 30 a Filin Jirgin Sama Ta Na Ƙoƙarin Shiga Jirgi da Su

    April 30, 2026

    A Wasan Hausa na koyi yadda ake sace Mutane – In ji Matashin da DSS suka kama a Kano

    February 13, 2026

    Duk wanda ya Kashe Wani a nemi shawarar Malamai a aika shi Lahira Kawai – Sheikh Daurawa

    January 18, 2026
  • Karin Wasu
    1. Kasuwanci
    2. Ilimi
    3. Nishadi
    4. Muhalli
    5. Lafiya
    6. Ra’ayi
    7. Wasanni
    8. View All

    PalmPay ya shiga Zukatan Yan Najeriya

    October 23, 2026

    Burin Palmpay Shine Kyautatawa Yan Najeriya

    October 19, 2026

    Kuna Daga Cikin Masu Kauracewa Ƙananan Takardun Kuɗin Najeriya?

    September 26, 2026

    Yara ’yan kasa da shekaru 13 sun fafata a gasar kwallon kafa da kamfanin Milo ya shirya a Kano

    September 22, 2026

    Yadda Na Taka Rawa Aka Mayar Da Malamai 12,000 Cikin Aji A Lokacin Ina Kwamishina — Hon. Sunusi Kiru

    October 25, 2026

    Masanin Kimiyyar Yanayi Daga Kano Dr. Salisu Ya Shiga Jerin Fitattun Masu Bincike na Duniya

    August 18, 2026

    Ya ce Yana Daukar Daliban A Matsayin ‘Ya ‘Yansa

    August 13, 2026

    Sabon Albashin Zai Fara Aiki A Watan Satumba

    August 10, 2026

    An Amince da Fara Shirya Fim ɗin Maitatsine – Darakta

    January 9, 2026

    Karamin Yaron da Kakarsa Ta yi Sanadiyar Daukakarsa a Duniya ya Cika Shekara 12

    December 14, 2025

    MUTU KA RABA — HISBA ta ce aure tsakanin Mai Wushirya da ‘Yar Guda ba ta dauke shi da wasa ba

    October 21, 2025

    Majalisar Yara: Gwamna Yusuf ya baiwa yara aron zaman majalisar zartaswarsa a Kano dan girmama Ilimi

    January 13, 2025

    Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar cin tarar kuɗi ga duk wanda ya sake tofar da yawu ko majina akan hanya

    February 3, 2025

    Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta dauki sabbin matakan kare Muhalli

    January 31, 2025

    Daga yanzu an daina barin tilin shara akan titunan birnin Kano – Gwamnatin Kano

    January 13, 2025

    YANZU YANZU :WHO Ta Ce Najeriya Ba Ta Da Mai Cutar Ebola Ko Mutum Daya A Halin Yanzu

    October 26, 2026

    Gwamnan ya kai Ziyarar ne Cikin Dare.

    August 16, 2026

    Likitoci Su Daina Ƙaura Zuwa Ƙasashen Waje, Najeriya Na Buƙatar Su – Dr. Habib

    July 23, 2026

    Da ’Yan Najeriya Sun San Haɗarin Abincin da Ake Shanyawa a Gefen Hanya, Ko Kyauta Aka Ba Su Ba Za Su Ci Ba — Masana

    January 30, 2026

    Ayyukan Gwamna Abba Babban Jari Ne Ga Mutanan Kano

    October 7, 2026

    Yaƙin siyasar Goje: Fafatawa da Tinubu, Gwamna Inuwa, Usman Kumo da ‘yan takarar APC gabanin 2027 – Engr. Ibrahim Suleiman Kashere

    September 29, 2026

    “ADC Ba Ta Da Karfin Kuri’a a Kudu maso Yamma, Atiku Ya Kamata Ya San Da Haka” — Hon Shehu Isah

    August 16, 2026

    Ya kamata Hisba da Malamai a Kano su bayyana matsayinsu kan yadda yan siyasa ke jifan juna da kalmar LUWADI – Anas Hassan

    February 24, 2025

    Burinmu a yanzu shine Barau FC ta samu gurbin shiga gasar zakarun Nahiyar Africa – DSP Barau

    February 25, 2025

    An karrama jagoran kwallon kafa na Barau Jibiril Academy da lambar gwarzon shekara a bangaren Shugabanci

    December 21, 2024

    YANZU YANZU :WHO Ta Ce Najeriya Ba Ta Da Mai Cutar Ebola Ko Mutum Daya A Halin Yanzu

    October 26, 2026

    Rikicin NDC: ’Yan Takarar Kano 5 Sun Kai Ƙara INEC, Sun Zargi Shugabannin Jam’iyya Da Hana Su Takara

    October 26, 2026

    SDP ta yi gargadi da kada a fake da Cutar Ebola a dage zaben 2027

    October 26, 2026

    Yadda Na Taka Rawa Aka Mayar Da Malamai 12,000 Cikin Aji A Lokacin Ina Kwamishina — Hon. Sunusi Kiru

    October 25, 2026
TST HAUSATST HAUSA
Home » Da ’Yan Najeriya Sun San Haɗarin Abincin da Ake Shanyawa a Gefen Hanya, Ko Kyauta Aka Ba Su Ba Za Su Ci Ba — Masana
Lafiya

Da ’Yan Najeriya Sun San Haɗarin Abincin da Ake Shanyawa a Gefen Hanya, Ko Kyauta Aka Ba Su Ba Za Su Ci Ba — Masana

By tstJanuary 30, 20263 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp
IMG 20260130 WA0001

Masana harkokin lafiya da noma sun sake jaddada gargadi kan al’adar shanya amfanin gona a gefen manyan hanyoyi a Najeriya, suna bayyana cewa dabi’ar na jefa lafiyar al’umma cikin hatsari tare da tauye ingancin abincin da jama’a ke ci a kullum.

A yawancin yankunan ƙasar nan musamman karkara da gefen manyan tituna, manoma kan shanya amfanin gona da suka hada da rogo da masara da shinkafa da wake da barkono da tumatir da albasa da Agushi a bakin hanya domin su bushe bayan girbe su daga gona.

KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/agwamnatin-tinubu-ta-janye-kiranta-ga-yan-najeriya-na-su-fara-azumin-kwana-uku-saboda-karancin-abinci-a-kasa/

TST Hausa ta rawaito cewa amfani da wannan hanya ta zama ruwan dare sakamakon talauci,da rashin kayan busarwa na zamani da kuma raunin kayan aikin bayan girbi.

Sai dai masana sun bayyana cewa, yayin da motocin da sauran ababan hawa ke wucewa a kan hanyoyi, kura mai ɗauke da hayakin mota,da datti da ƙananan sinadarai masu cutarwa na sauka kai tsaye kan wadannan amfanin gona.

Sun ce hakan na iya janyo gurɓatewar kayan abincin sannan ƙwayoyin cuta ka iya shiga musamman kananan ƙarafa da ido baya iya gani da wasu sinadarai da ke iya illata lafiyar dan Adam.

A cewar masana, ci gaba da cin irin wannan abinci na dogon lokaci na iya haddasa matsalolin lafiya musamman ga yara,da mata masu juna biyu da tsofaffi, ko da kuwa ba a ganin illa nan take.

Sun kuma nuna cewa wannan dabi’a na iya ƙara yawaitar cututtuka da ba a gano musabbabinsu da wuri.

A wurare da dama da ake shanya amfanin gona, a kan hango awakai da kaji suna yawo suna taka su.

Wannan yanayi ya ƙara nuna irin barazanar tsafta da ke tattare da al’adar busar da kayan gona a bakin hanya.

Wata masaniyar abinci mai gina jiki, Mrs. Helen Okorie, ta bayyana matuƙar damuwa kan lamarin, inda ta ce duk lokacin da dabbobi suka taka ko suka yi mu’amala da abinci, suna shigar da ƙwayoyin cuta, tsutsotsi da kuma najasa, abin da ke mayar da abincin haɗari ga lafiyar dan Adam.

Ta bayyana cewa cin irin wannan abinci na iya haddasa cututtuka iri-iri, musamman ga yara, mata masu juna biyu da tsofaffi, tare da kira ga manoma da ’yan kasuwa da su ɗauki hanyoyin busarwa masu tsafta domin kare lafiyar jama’a.

KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/farashin-kayan-abinci-ya-sauka-sosai-amma-takin-zamani-da-zamuyi-amfani-da-shi-yanzu-yafi-karfinmu-manoma/

Baya ga barazanar lafiya, masana sun ce shanya amfanin gona a bakin hanya na rage daraja,da tsafta da ingancin kayan gona, lamarin da ke hana su cika ƙa’idojin tsaron abinci da ake bukata a manyan kasuwanni da ma kasashen waje.

Wannan na kawo cikas ga bunƙasar kasuwancin noma da ƙoƙarin fitar da kayan gona zuwa waje.

Masana sun shawarci manoma da ’yan kasuwa da su daina amfani da bakin hanya wajen busar da amfanin gona, su koma hanyoyi masu aminci kamar rumfunan busarwa, tabarmomi da aka ɗaga daga ƙasa, ko injinan busarwa na zamani. Sun kuma yi kira ga gwamnati a matakai daban-daban, tare da ƙungiyoyi masu zaman kansu, da su zuba jari a fannin kayan aikin bayan girbi, domin kare lafiyar jama’a, rage asarar amfanin gona da inganta harkar noma a Najeriya.

Share. Facebook Twitter Email Telegram WhatsApp

Related Posts

YANZU YANZU :WHO Ta Ce Najeriya Ba Ta Da Mai Cutar Ebola Ko Mutum Daya A Halin Yanzu

October 26, 2026

Gwamnan ya kai Ziyarar ne Cikin Dare.

August 16, 2026

Likitoci Su Daina Ƙaura Zuwa Ƙasashen Waje, Najeriya Na Buƙatar Su – Dr. Habib

July 23, 2026

WHO Ta Yi Kira Da A Kara Haraji Kan Barasa Da Abubuwan Sha Masu Dauke Da Sikari

January 14, 2026
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

YANZU YANZU :WHO Ta Ce Najeriya Ba Ta Da Mai Cutar Ebola Ko Mutum Daya A Halin Yanzu

October 26, 2026

Rikicin NDC: ’Yan Takarar Kano 5 Sun Kai Ƙara INEC, Sun Zargi Shugabannin Jam’iyya Da Hana Su Takara

October 26, 2026

SDP ta yi gargadi da kada a fake da Cutar Ebola a dage zaben 2027

October 26, 2026

Yadda Na Taka Rawa Aka Mayar Da Malamai 12,000 Cikin Aji A Lokacin Ina Kwamishina — Hon. Sunusi Kiru

October 25, 2026

Sai Shekarar 2031 Za Mu Bar Villa – Remi Tinubu

October 24, 2026
Advertisement
© 2026 TST HAUSA Developed by ENGRMKS & CO..
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.