Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da tuhume-tuhume guda takwas da Gwamnatin Tarayya ta shigar kan Adeniyi Adeyemi, wanda ake zargi da ƙirƙirar kansa a matsayin Darakta-Janar na Hukumar Tallata Shiga Tsakani ta Ƙasashen Waje ta Fadar Shugaban Ƙasa.
Mai shari’a Mohammed Garba Umar ne ya yanke hukuncin bayan Gwamnatin Tarayya ta nemi a dakatar da shari’ar, tana mai cewa za a mayar da Adeyemi zuwa Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya domin sake gurfanar da shi.
Daraktan Masu Gabatar da Ƙara na Tarayya, Rotimi Oyedepo, SAN, ya shaida wa kotun cewa Ministan Shari’a kuma Antoni-Janar na Tarayya ya sake duba takardun shari’ar, tare da gano wasu kura-kurai a cikin tuhume-tuhumen da Sufeto-Janar na ’Yan Sanda ya fara shigarwa.
Ya ce laifukan da ake zargin Adeyemi da aikatawa na ƙirƙirar takardun bogi sun fi dacewa a gurfanar da su a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya maimakon Babbar Kotun Tarayya.
Oyedepo ya ƙara da cewa an riga an shigar da sabbin tuhume-tuhume a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya, kuma za a sake gurfanar da Adeyemi ba tare da ɓata lokaci ba.
Lauyan Adeyemi, Ibrahim Angulu, SAN, bai yi hamayya da wannan buƙata ba, lamarin da ya sa mai shari’a Umar ya yi watsi da ƙarar.
Adeyemi mai shekaru 38, yana fuskantar shari’ar tare da wasu mutane biyu da ake zargi da haɗa baki da ƙirƙirar takardun bogi.
An bayyana sunayen mutanen biyu a matsayin Femi da Anu, amma har yanzu ba a san cikakken sunayensu ko inda suke ba.

