Wani sabon shirin gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas na kafa kamfanin jirgin sama na yanki ya ƙara ƙarfafa ra’ayin gwamnatin Kano na kafa nata kamfanin jirgin sama na kasuwanci mai suna Kano first Airline.
Wani masani kan harkokin manufofin gwamnati da tattalin arziki, Sanusi Kiru, ya bayyana cewa shirin na Arewa maso Gabas ya nuna yadda jiragen sama za su iya zama muhimmin ɓangare na bunƙasa tattalin arziki da haɗa yankuna.
Sanusi Kiru ya bayyana hakan ne a wani sabon rubutu da ya yi kan shirin kafa kamfanin jirgin sama na Kano, inda ya ce ci gaban da aka samu a Arewa maso Gabas ya ƙara tabbatar da hujjar da ya gabatar tun watan Yunin 2026.
A cewarsa, jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe sun haɗa kai wajen kafa kamfanin jirgin sama na yanki, da nufin sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki tare da bunƙasa kasuwanci a yankin.
Rahotannin da ya ambata sun nuna cewa jihohin shida sun amince da samar da kusan Naira biliyan 30, inda kowace jiha za ta bayar da Naira biliyan 5, yayin da aka ce tuni an samu kusan Naira biliyan 10.8.
Sanusi Kiru ya ce wannan ci gaba ya dace da hujjar da ya gabatar a baya cewa shirin Kano na kafa kamfanin jirgin sama bai kamata a kallesa a matsayin wani aikin nuna isa kawai ba, sai dai a matsayin wani muƙamin dabarun bunƙasa tattalin arziki.
Ya ce Kano na da dalilai masu ƙarfi da za su sa irin wannan kamfani ya samu damar yin aiki, musamman saboda yawan jama’ar jihar, matsayinta na babbar cibiyar kasuwanci a Arewa, harkokin noma da kuma alaƙar kasuwancinta da sauran jihohi da ƙasashen makwabta.
Jirgin sama zai taimaka wajen kasuwanci da noma
Sanusi Kiru ya ce muhimmancin shirin ya wuce jigilar fasinjoji, domin jiragen sama na iya taimakawa wajen jigilar kayan amfanin gona da sauran kayayyakin kasuwanci cikin sauri.
Ya bayyana cewa kayan amfanin gona masu saurin lalacewa na buƙatar tsarin sufuri mai sauri domin kai su kasuwannin da suke da daraja, kuma hakan na iya bai wa manoma da ‘yan kasuwa damar samun sabbin kasuwanni.
Ya ce idan aka haɗa harkar jiragen sama da sarkar samar da kayayyaki, ajiyar kaya, tantance ingancin kayayyaki da kayayyakin more rayuwa na fitar da kaya zuwa ƙasashen waje, Kano za ta iya amfani da filin jirginta wajen ƙara bunƙasa kasuwanci da noma.
Kano na da damar zama cibiyar jiragen sama a Arewa
Marubucin ya kuma bayyana cewa tattalin arzikin Kano yana da alaƙa da sassan Arewa da ƙasashe makwabta, abin da ya ce zai iya bai wa kamfanin jirgin saman Kano damar samun kasuwa mai faɗi.
Ya ce kamfanin da aka kafa a Kano zai iya samar da hanyoyin jiragen sama zuwa muhimman cibiyoyin kasuwanci, tare da ƙara ƙarfafa matsayin jihar a matsayin cibiyar kasuwanci da jigilar kayayyaki.
Sai dai ya jaddada cewa nasarar shirin za ta dogara ne da yadda za a gudanar da kamfanin.
A cewarsa, bai kamata a gudanar da kamfanin jirgin saman kamar wata ma’aikatar gwamnati ba, domin harkar na buƙatar ƙwararrun ma’aikata, gaskiya wajen sayayya, ingantaccen tsarin gudanar da kuɗi, hanyoyin jiragen da za su iya kawo riba, jiragen da suka dace da kuma tsauraran matakan tsaro.
Ya kuma ba da shawarar a duba damar haɗa kamfanoni masu zaman kansu da sauran masu zuba jari wajen gudanar da shirin, domin tabbatar da dorewarsa.
Ya kamata Kano ta koma matakin aiwatarwa
Sanusi Kiru ya ce sabon shirin jihohin Arewa maso Gabas ya ƙara nuna cewa akwai buƙatar Kano ta ci gaba da shirin nata, amma ta gudanar da shi bisa tsarin kasuwanci mai inganci.
Ya ce abin da ya kamata a mayar da hankali a kai yanzu shi ne gudanar da bincike mai zurfi kan yiwuwar shirin, samar da tsarin kasuwanci, da kuma tabbatar da cewa kamfanin zai iya dogaro da kansa ba tare da zama nauyi ga gwamnatin jihar ba.
Ya ce manufar ba wai kawai ta kasance mallakar jiragen sama ba ce, illa samar da kamfanin jirgin sama mai ɗorewa wanda zai taimaka wajen dawo da Kano matsayinta na ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci da tattalin arziki na Najeriya.
A cewarsa, ci gaban shirin Arewa maso Gabas ya zama wani sabon ƙarin dalili da ke ƙarfafa ra’ayin cewa Kano na da damar amfani da harkar sufurin jiragen sama wajen bunƙasa kasuwanci, noma, zirga-zirga da haɗin kan tattalin arzikin yankin.

