Kamfanin hada-hadar kuɗi na zamani na PalmPay ya gargaɗi kwastomominsa da su ƙara taka-tsantsan wajen kare bayanan asusunsu, musamman daga masu damfara da ke kwaikwayon jami’an kula da kwastomomi domin satar kuɗi ko samun damar shiga asusun mutane.
Kamfanin ya bayyana cewa, yayin da al’ummar Najeriya ke ƙara dogaro da manhajojin hada-hadar kuɗi wajen gudanar da harkokinsu na yau da kullum, sanin sahihan hanyoyin neman taimako ya zama muhimmin mataki wajen kare kai daga zamba da asarar kuɗi.
PalmPay ya ce wasu daga cikin masu damfarar kan yi amfani da kiran waya ko saƙonnin intanet, suna gabatar da kansu a matsayin ma’aikatan kamfanin, tare da yin alkawarin kyaututtuka ko mayar da kuɗi, ko kuma ikirarin cewa suna son taimakawa wajen warware matsalar asusu.
Sai dai kamfanin ya jaddada cewa bai kamata kwastomomi su bayyana lambobin sirri na tabbatar da hada-hadar kuɗi (OTP), lambobin PIN, kalmomin sirri ko wasu bayanan tsaro ga wani mutum ba, ko da kuwa ya gabatar da kansa a matsayin jami’in kamfanin.
Haka kuma, ya shawarci kwastomomi da su guji danna hanyoyin intanet da ake zargin ba su da inganci, tare da tabbatar da sahihancin duk wani saƙo ko buƙatar bayanai kafin ɗaukar mataki.
A ɓangaren ’yan kasuwa kuwa, PalmPay ya jaddada muhimmancin tabbatar da cewa kuɗi sun shiga asusu ta hanyar duba bayanan hada-hadar kuɗi kai tsaye a manhajarsu, maimakon dogaro da hoton shaidar biyan kuɗi ko saƙon da aka turo musu, wanda zai iya zama na bogi.
Hanyoyin tuntuɓar PalmPay na hukuma
Kamfanin ya bayyana cewa kwastomomin da ke buƙatar taimako kan asusunsu, waɗanda suka gano wata hada-hadar kuɗi da ba su sani ba, ko kuma suke zargin an yi yunƙurin damfararsu, za su iya tuntuɓar PalmPay ta hanyoyin da ya tanada.
Hanyoyin sun haɗa da kiran waya ta lamba 0201 888 6888, aika saƙon imel zuwa support@palmpay.com, ziyartar shafin www.palmpay.com ko amfani da sashen tattaunawa da jami’an kula da kwastomomi kai tsaye da ke cikin manhajar PalmPay.
PalmPay ya kuma ƙarfafa masu amfani da manhajarsa da su fahimci hanyoyin tsaro da ke cikin sashen Security Center, su adana sahihan bayanan tuntuɓar kamfanin, tare da gaggauta kai rahoton duk wani abu da suke zargin ba shi da inganci.
Kamfanin ya ce zai ci gaba da wayar da kan kwastomomi kan hanyoyin kare kuɗaɗensu da kauce wa damfara ta hanyar kamfen ɗinsa na wato PalmPay Dey For You, tare da inganta hanyoyin samun taimako domin masu amfani da manhajar su iya samun sahihin bayani a duk lokacin da suke buƙata.

