Babban kwamandan hukumar Hisba ta jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya nuna takaicinsa kan yadda ake gaza daukar hukuncin Kisa akan masu kashe mutane da gan gan.
Malamin ya ce kisan kai na daga cikin manyan laifuka da Musulunci ya haramta, tare da bayyana wasu muhimman dalilai guda hudu da ke kara haddasa yawaitar aikata kisa a cikin al’umma.
Sheikh Daurawa a yayin hira da Rahma Radio kai tsaye ta wayar salula game da abinda ke faruwa a Kano da wasu jihohin Arewa ya ce kashe wani ba tare da hakkin shari’a ba, hukuncinsa babba ne a wajen Allah, kuma shawarar malamai ita ce a bar hukuncin ya yi aiki akansa.
Malamin ya ce daga cikin manyan abubuwan da ke janyo karuwar kisan kai akwai rashin daukar hukuncin kisa kan wanda ya aikata kisa, yana mai cewa idan ba a hukunta masu laifi yadda ya kamata ba, hakan na kara musu karfin guiwar aikata laifi, tare da haddasa rashin tsoron doka a cikin al’umma.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/matashin-da-ya-jagoranci-taaddancin-dorayi-shine-ake-zargi-da-kone-mata-biyu-a-tudun-yola-in-ji-yan-sanda/
Daga nan Sheikh Daurawa ya kara da cewa rashin ilimi, musamman na addini, na daga cikin manyan dalilan da ke janyo mutane aikata kisan kai, domin jahilci kan koyarwar addini yana sa mutum ya raina darajar rayuwar dan Adam.
Haka kuma, malamin ya yi nuni da shaye-shaye a matsayin wani babban abin da ke janyo aikata kisa, yana mai bayanin cewa yanayi na maye kan gusar da hankali da tunani, sannan ya janyo mutum aikata abubuwan da ba zai taba yi a cikin hayyacinsa ba.
Kazalika, Sheikh Daurawa ya ce yawan kallon wasannin kwaikwayo da fina-finai masu dauke da tashin hankali na taka rawa wajen karfafa dabi’ar kisa, musamman a tsakanin matasa, saboda suna koya musu daukar tashin hankali a matsayin abin nishadi ko mafita ga matsaloli.
A karshe, Sheikh Daurawa ya yi kira ga hukumomi, musamman gwamnoni da su rika aiwatar da hukuncin Kisa akan masu kashe mutane sannan malamai, da iyaye da al’umma baki daya su hada kai wajen yaki da wadannan matsaloli ta hanyar daukar hukunci cikin adalci, inganta ilimi, yaki da shaye-shaye, da kuma kula da abubuwan da ake nunawa yara da matasa, domin samar da zaman lafiya mai dorewa a cikin kasa.

