Majalisar Zartarwar Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta amince da kashe jimillar Naira biliyan 55.475 domin aiwatar da manyan ayyukan raya kasa da shirye-shiryen inganta rayuwar al’ummar jihar.
Kwamishinan yada labarai da Al’amuran cikin gida na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya ya shaida hakan ga manema labarai na fadar gwamnatin Kano bayan kammala Zaman majalisar.
A taron majalisar karo na 40 da aka gudanar a ranar 22 ga Yulin 2026, majalisar ta ce kudaden za su tafi ne wajen bunkasa bangarorin ilimi, lafiya, hanyoyi, samar da ruwan sha, muhalli, gidaje, raya karkara, yada labarai da sauran muhimman fannoni.
Bangaren Ilimi shi ne ya fi samun kaso mafi tsoka, inda aka amince da gyare-gyare da gina sabbin gine-gine a makarantu da dama, samar da kujeru da tebura, dakunan ICT, dakunan karatu, tsarin hasken rana, motocin makarantu da kuma biyan bashin abincin daliban makarantun kwana.
Kwamishinan yace a bangaren lafiya, an amince da sake gina da inganta cibiyoyin kiwon lafiya, samar da sabbin kayan aikin asibitoci, kayan daki da kuma fadada wasu cibiyoyin lafiya a fadin jihar.
Haka kuma, majalisar ta amince da biyan diyya ga masu gidaje da filayen da manyan ayyukan gina hanyoyi suka shafa, ciki har da Kano Northern Bypass da sauran hanyoyin da ake fadadawa.
A bangaren ruwa da muhalli, an ware biliyoyin naira domin samar da man dizal ga cibiyoyin samar da ruwa, biyan kudin wutar lantarki, share magudanan ruwa, gyaran makabarta, kawata wuraren shakatawa da kuma gina sabbin magudanan ruwa a Gwale.
A bangaren ayyuka (Works) kuwa, an amince da gina da gyaran manyan hanyoyi, samar da hasken tituna na zamani masu amfani da hasken rana, gyaran gine-ginen gwamnati da kuma wasu manyan ayyukan more rayuwa.
Majalisar ta kuma amince da gina katanga a Kwankwasiyya City da Amana City, bayar da tallafin aikin RAAMP da aiwatar da sabon shirin raya karkara na tsawon shekara biyar.
A bangaren yada labarai, an amince da sayen sabbin kayan aikin KSBC, horas da jami’an yada labarai da kuma gyaran ofishin Kwamishinan Yada Labarai.
Har ila yau, majalisar ta amince da tura wasu kudurorin dokoki ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin inganta bangaren lafiya da cibiyoyin horas da ma’aikatan lafiya.
Majalisar ta kuma amince da shiga shirin NG-CARES 2.0 domin fadada shirye-shiryen tallafa wa masu karamin karfi da bunkasa tattalin arzikin al’umma.
Baya ga haka, majalisar ta ayyana abin da aka fi sani da “Daba” a matsayin mummunar dabi’a tare da umurtar hukumomin tsaro su dauki matakan dakile ta.
Haka kuma, majalisar ta yaba da nasarar aikin Hajjin 2026 na Alhazan Kano, sannan ta saurari gabatarwa kan tattalin arzikin Halal na duniya, tare da bayyana aniyar Kano ta zama cibiyar kasuwancin Halal.
A yayin taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karbi lambobin yabo da dama daga kungiyoyi daban-daban saboda irin nasarorin da gwamnatinsa ke samu a bangarorin ilimi, lafiya, ababen more rayuwa da kyakkyawan shugabanci.
Majalisar ta ce wadannan amincewa da ayyuka na nuna kudirin gwamnatin Kano na ci gaba da samar da ci gaba mai dorewa da inganta rayuwar al’ummar jihar.

