Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Lokoja, Jihar Kogi, ta soke hukuncin da ta yanke a baya wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi wa Jam’iyyar NDC rajista a matsayin jam’iyyar siyasa.
Mai shari’a Justice Isah Dashen ya ce an samu kura-kurai a shari’ar farko, domin ba a bai wa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa damar gabatar da hujjojinsu ba kafin yanke hukunci.
Saboda haka, kotun ta jingine hukuncin gaba ɗaya tare da ba da umarnin a sake fara sauraron ƙarar daga tushe.
Kotun ta bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan dalilan soke hukuncin shi ne korafin da Jam’iyyar Peace Movement Party (PMP) ta shigar, inda ta ce tambarin da NDC ke son amfani da shi nata ne. Sai dai ba a haɗa PMP a cikin shari’ar tun farko ba, lamarin da kotun ta ce ya sa ba a yi cikakken adalci ba.
Da wannan hukunci, umarnin da ya tilasta wa INEC yin rajistar NDC ya daina aiki nan take. Yanzu kotun za ta sake sauraron shari’ar tare da bai wa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa damar gabatar da hujjojinsu kafin ta yanke sabon hukunci.
Hukuncin na nufin cewa har sai an kammala sabon sauraron shari’ar, jam’iyyar NDC ba ta da cikakkiyar shaidar zama halastacciyar jam’iyyar siyasa a Najeriya.

