Gwamnatin jihar Kano, ta sanar da kaddamar da wani sabon dandali da gwamnatin jihar ta samar domin inganta daidaito da tsari a yada manufofi da shirye-shiryen gwamnati, tare da dakile rudani ko sabanin bayanai a manyan makarantun gaba da sakandire a jihar.
Kwamishinan ma’aikatar yada labarai da al’amuran cikin gida na jihar Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan a yayin ganawarsa da manema labarai a ofishinsa, lokacin kaddamar da kwamatin wanda ya hada da jami’an hulda da jama’a na makarantun gaba da sakandire a jihar.
Yace ayyukan cigaban ilimi a kano ya wuce zato, musamman idan akayi la’akari da fifikon da Gwamna Yusuf yake baiwa Bangaren a duk shekara cikin kasafin kudi.
Ya kara da cewa inda ya ce manufar Samar da dandalin shine domin samar da sahihin bayani cikin tsari da kwarewa da kuma tallata ayyukan gwamnati.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/za%c9%93en-cike-gurbi-a-kano-ya-tabbatar-da-sauyin-salo-a-siyasar-jihar-gwamna-yusuf/
A cewarsa, taron ya fi mayar da hankali kan muhimman batutuwa guda biyu da suka hadar da karfafa hadin gwiwa tsakanin ma’aikatar da jami’an hulda da jama’a na manyan makarantu, domin tabbatar da cewa bayanan da ake fitarwa sun kasance daidai, sahihai kuma cikin tsarin da ya dace.
Sai kuma abinda ya shafi fadakar da jama’a kan nasarorin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta samu a bangaren ilimi mai zurfi tun bayan hawanta karagar mulki.
Waiya ya ce a karkashin jagorancin gwamnan, an samu ci gaba mai ma’ana a fannin manyan makarantu a fadin jihar. Ya ce daga cikin ayyukan da aka aiwatar akwai gyaran tsofaffin gine-gine, gina sababbin azuzuwa da ofisoshi, samar da kayayyakin koyarwa na zamani, horas da ma’aikata, da kuma daukar matakan inganta ka’idoji da tsarin gudanar da ilimi.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/gwamna-yusuf63-kana-mulkar-kanawa-akan-irin-akidar-malam-aminu-kano-cikin-tausayi-tinubu/
Ya kara da cewa gwamnatin mai ci ta kuduri aniyar dawo da martaba da kimar manyan makarantu ta hanyar samar da ingantaccen yanayin koyo da koyarwa, tare da magance matsalolin da suka dade suna tarnaki ga ci gaban wadannan cibiyoyi.
A karshe, kwamishinan ya bukaci jami’an hulda da jama’a na cibiyoyin ilimi da su kara zage damtse wajen yada ayyukan gwamnati cikin gaskiya da kwarewa, yana mai jaddada cewa sadarwa mai inganci ita ce ginshikin tabbatar da fahimtar jama’a kan manufofi da tsare-tsaren gwamnati.

