Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kudirin gwamnatinsa na kafa Hukumar Kula da Mahauta ta Jihar Kano domin tsara harkokin sana’ar fawa, bunkasa ta, da kuma kare muradun masu gudanar da wannan sana’a a fadin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani taron da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano, inda ya kaddamar da shirin tallafa wa mahauta 1,900 da kayan aikin inganta sana’arsu.
TST Hausa ta rawaito cewa kayan da aka tallafawa mahautan sun hada da Gatari da Daro da Faranti da Wuka da sauransu.
Ya ce kafa wannan hukuma na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke dauka na inganta harkokin kasuwanci da sana’o’in dogaro da kai, tare da samar da yanayi mai kyau da zai ba mahauta damar gudanar da ayyukansu cikin tsari da inganci.
Ya shaida cewa samar da hukumar zaisa a tsaftace sana’ar Fawa a jihar.
A yayin taron, Gwamna Yusuf ya kuma sanar da bayar da tallafin kudi na naira miliyan 100 ga kungiyar mahauta, inda ya ce za a raba kudin domin tallafa musu wajen fadada sana’o’insu, bunkasa kasuwancinsu, da kuma inganta rayuwarsu.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bullo da shirye-shiryen da za su karfafa tattalin arzikin al’umma, musamman ta hanyar tallafa wa kungiyoyi da masu sana’o’i daban-daban domin samar da ayyukan yi da rage talauci.
Mahautan da suka amfana da tallafin sun yabawa gwamnatin jihar bisa wannan mataki, tare da bayyana cewa tallafin zai taimaka matuka wajen inganta sana’arsu da kuma kara habaka harkokin kasuwancinsu.

