An sako matafiya 28 da aka yi garkuwa da su a hanyar zuwa taron Maulidi a garin Zak da ke yankin Bashar a Karamar Hukumar Wase ta Jihar Filato.
A ranar 21 ga Disamba, 2025, ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Zak da ke yankin Bashar a Ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato.
Mutanen da aka sace maza da mata da kuma yara na kan hanyarsu ta zuwa garin Sabon Layi, a yankin Bashar din, domin halartar bikin Mauludi, lokacin da aka tare su aka yi garkuwa da su.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/namadi-dala-ya-taya-alummar-musulmi-murnar-shigowar-watan-mauludi/
Bayan sace su, masu garkuwa da mutanen sun tuntubi ’yan uwansu, suna buƙatar a biya kuɗin fansa na Naira miliyan daya da rabi kowane mutum.
’Yan uwan sun ce ba su da ikon biyan kuɗin, suka roki a sako mutanen.
Daga baya masu garkuwa da mutanen sun rage kuɗin fansar zuwa Naira miliyan 30, amma suka ƙara bukatar a kawo sabbin babura uku kacal.
A ranar Alhamis kuma, iyalan wadanda aka sace sun ce masu garkuwa da mutanen sun sake sauya sharadi, inda suka buƙaci Naira miliyan 1da dubu dari biyar da kuma sabon babur daya kan kowane mutum kafin sakinsa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/sakon-obasanjo-ga-tinubu-abin-kunya-ne-gwamnati-mai-%c6%99arfin-iko-ta-rika-sulhu-da-%c6%b4an-bindiga/
Har yanzu ba a tabbatar ko an biya kuɗin fansa ba, sai dai iyaye sun ce ko sisin kwabo ba su biya ba.
Waɗanda aka sace sun shafe kwanaki 20 a hannun masu garkuwa da mutane kafin a sako su.

