Babban limamin Masallacin Usman bn Affan da ke unguwar Gadon Kaya a Karamar Hukumar Gwale ta Jihar Kano, Dr. Aliyu Yunus Muhammad ya yi kira ga Musulmi da su kiyaye iyakokin da addinin Musulunci ya gindaya game da wasiyya, yana mai jaddada cewa ba duk wata wasiyya da mamaci ya bari ake aiwatarwa ba idan ta ci karo da koyarwar Alƙur’ani da Sunnah
Malamin ya bayyana hakan ne yayin hudubar Juma’a da ya gabatar a masallacin, inda ya ce Musulunci ya yi umarni da cika halastacciyar wasiyya, amma ya haramta aiwatar da duk wata wasiyya da ta saɓa wa Shari’a.
A cewarsa, daga cikin abubuwan da ba ya halatta a aiwatar ko da mamaci ya yi wasiyya da su akwai:
1.Yin wasiyya da abin da Allah Ya haramta, kamar tallafawa saɓo ko wani aiki da ya saɓa wa Musulunci.
2.Yin wasiyya ga magaji, sai idan duk sauran magada sun amince bayan rasuwarsa.
3.Yin wasiyya da ta wuce kashi ɗaya bisa uku (1/3) na dukiyarsa, sai idan magada sun amince.
4.Canja rabon gado da Allah Ya tanada a cikin Alƙur’ani.
5.Hana wani magaji haƙƙinsa na gado ko ƙoƙarin tauye rabonsa.
6.Barin bashin mutane ba tare da an biya ba, ko yin umarnin kada a biya bashin da ake binsa.
7.Yin umarni da ayyukan bidi’a da ba su da tushe a Alƙur’ani da Sunnah.
8.Yin umarni a gina kabari cikin alfahari, ko yin abubuwan da suka saɓa da yadda Musulunci ya koyar game da kaburbura.
9.Yin wasiyyar da manufarta ita ce cutar da magada ko jefa sabani a tsakaninsu.
10.Yin wasiyyar zaman makoki, ko umarnin a rika gudanar da zaman makoki na kwanaki uku, bakwai, arba’in ko shekara, yana mai cewa wannan ba ya halatta idan ana ɗaukarsa a matsayin wani tsari na addini.
Dr. Aliyu Yunus ya ce abin da Musulunci ya koyar bayan rasuwar mutum shi ne a yi masa jana’iza kamar yadda Shari’a ta tanada, a yi masa addu’a da neman gafara, a biya bashinsa idan yana bi, a aiwatar da halastacciyar wasiyyarsa, sannan a raba dukiyarsa tsakanin magada kamar yadda Allah Ya shar’anta.
Ya bukaci Musulmi su guji ɗaukar al’adu a matsayin ibada, tare da neman ilimin addini daga malamai amintattu domin tabbatar da cewa ibadunsu da mu’amalolinsu sun dace da koyarwar Alƙur’ani da Sunnah.

