Tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Hon. Muhammad Sanusi Sunusi Kiru, ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cancanci cikakkiyar kuri’ar amincewa kan irin gagarumar nasarar da gwamnatinsa ta samu wajen farfaɗo da bangaren ilimi a jihar.
A wata makala da ya wallafa, Kiru ya ce duk da bambancin ra’ayin siyasa, gaskiya da adalci sun wajabta a yaba wa gwamnati idan ta yi abin a yaba.
Ya ce bayan nazarin ayyukan gwamnatin tsakanin shekarun 2024 zuwa 2026, musamman kokarin magance matsalar karancin malamai, ya gamsu cewa gwamnatin ta samu gagarumar nasara.
Ya bayyana cewa daya daga cikin manyan kalubalen da suka dade suna addabar ilimin Kano shi ne karancin malamai, wanda ya haifar da cunkoso a azuzuwa tare da rage ingancin koyarwa da koyo.
A cewarsa, gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta dauki matakin da ba a taba ganin irinsa ba, inda ta dauki ko ta tabbatar da aikin malamai 8,715 na dindindin, sannan ta dauki malamai 3,688 na wucin-gadi karkashin shirin BESDA Cohort V, lamarin da ya kai adadin malamai 12,403.
Ya kara da cewa idan aka hada da wadanda sauran hukumomin ilimi suka dauka, jimillar ta kai kusan malamai 13,000.
Kiru ya ce wannan na daga cikin mafi girman daukar malamai a tarihin Jihar Kano, kuma wani babban jari ne da aka zuba domin inganta makomar ilimin yara da ci gaban jihar baki daya.
Ya ce daukar sabbin malaman ya rage gibin da ake fama da shi a makarantu, ya kara inganta koyarwa, tare da tabbatar da cewa azuzuwa sun samu isassun malamai.
Haka kuma, ya ce rahotannin sa ido, kididdigar makarantu da bayanan hukumomin ilimi sun fara nuna alamun ci gaba a bangaren.
Ya kara da cewa idan za a yi hukunci bisa ayyukan da aka aiwatar maimakon siyasa, gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta cancanci yabo saboda irin ci gaban da ta samar a bangaren ilimi.
Sai dai ya shawarci gwamnati da ta kara karfafa bangaren yada labarai domin jama’a su kara fahimtar dimbin nasarorin da ake samu a sassa daban-daban na gwamnati.
Dangane da bikin mika takardun aiki ga sabbin malaman da aka dauka, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf zai jagoranta ranar Talata, 21 ga Yulin 2026, Kiru ya ce wannan ba bikin rabon takardun aiki kadai ba ne, illa wata alama ce ta sabon fata ga dubban iyalai da kuma tabbatar da kudirin gwamnati na samar da ingantaccen ilimi ga kowane yaro a Jihar Kano.
Ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya ci gaba da bai wa Gwamnan hikima, lafiya da karfin guiwa domin dorewa kan wannan kyakkyawan tsari na bunkasa ilimi.
A karshe, Hon. Muhammad Sanusi S. Kiru ya sake jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya cancanci yabo da cikakkiyar kuri’ar amincewa kan irin gagaruman sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo a bangaren ilimi.
Ya ce idan aka ci gaba da daukar malamai da zuba jari a ilimi, wannan zai kasance daya daga cikin manyan abubuwan da za su zama tarihi a mulkin Gwamnan, tare da sauya alkiblar ilimin Jihar Kano zuwa mafi kyawu.

