Close Menu
  • Shafin Farko
  • Labarai
  • Ketare
  • Siyasa
  • Noma da Kiwo
  • Yanayi
  • Tsaro
  • Karin Wasu
    • Kasuwanci
    • Ilimi
    • Nishadi
    • Muhalli
    • Lafiya
    • Ra’ayi
    • Wasanni
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp Telegram
TST HAUSATST HAUSA
  • Shafin Farko
  • Labarai

    Malaman Addinin Musulunci Daga Jihohin Arewa 19 Sun Goyi Bayan Tazarcen Tinubu A 2027

    August 23, 2026

    Hukumar Shari’a ta Kano Ta Wayar da Kan Jama’a Muhimmancin Kalandar Musulunci

    August 22, 2026

    Tinubu ya bada hutu Albarkacin ranar Haihuwar Annabi Muhammadu SAW

    August 21, 2026

    Tunda Farko dama Tinubu ya nemi INEC tayi Adalci.

    August 16, 2026

    HUDUBA : “Na Rantse da Allah, Allah Zai Tambayi ’Yan Kasuwa Kan ’Ya’yansu Saboda Rashin Ba Su Lokaci” — Dr. Abdullah Gadon Kaya

    August 14, 2026
  • Ketare

    Yau Ake Toshe Shafukan Sada Zumunta na Yara yan Kasa da Shekara 16 a Australia

    December 4, 2025

    Rikicin Gaza:Sarkin Saudiyya ya amincewa Falasdinawa 1000 su shiga kasar su sauke farali kyauta

    May 19, 2025

    Duk wanda ya yarda zai bar Amurika ya koma kasarsa zamu bashi kyautar Dala 1000 – Inji Trump

    May 6, 2025

    Ba a ga jinjirin watan Shawwal a Saudiyya ba

    March 29, 2025

    An ga watan Sallah karama a Saudiyya

    March 29, 2025
  • Siyasa

    Wasu ‘Yan Siyasa a Kano Sun Shawarci Kwankwaso Ya Koma PRP Ko Ya Huce Haushi

    June 26, 2026

    Kotu ta soke hukuncin da Ya bai wa NDC matsayin halastacciyar Jam’iyyar Siyasa a Najeriya

    June 26, 2026

    Jar Hula Dai Ta Malam Aminu Kano Ce, Don Haka Ba Za Mu Cire Ta Ba — Gwamna Yusuf

    June 25, 2026

    Na Rungumi Kaddara kan Rasa Takarar Kujerar Majalisar Tarayya a Gezawa da Gabasawa – Hon. Dan Malam

    May 8, 2026

    Kofa Har Yanzu a Buɗe Take ga Kwankwaso Ya Koma PRP, Tunda Akwai Shakkun Samun Mafita a NDC – In Ji Ali Rabiu Ali

    May 4, 2026
  • Noma da Kiwo

    Za’a samu ƙarancin shinkafar Basmati da Indiya ke nomawa a bana

    September 4, 2025

    Tsadar rayuwa: Komai matsayin mutum a Najeriya ya koma gona,saboda abinda na hango -Inji wani Lauya

    December 15, 2024
  • Yanayi
  • Tsaro

    Yan Bindiga Sunyi garkuwa da ’yan uwan Mataimakin Gwamnan Sokoto

    May 1, 2026

    An Kama Budurwa da Kunkuru 30 a Filin Jirgin Sama Ta Na Ƙoƙarin Shiga Jirgi da Su

    April 30, 2026

    A Wasan Hausa na koyi yadda ake sace Mutane – In ji Matashin da DSS suka kama a Kano

    February 13, 2026

    Duk wanda ya Kashe Wani a nemi shawarar Malamai a aika shi Lahira Kawai – Sheikh Daurawa

    January 18, 2026

    An sako Yan Mauludi 28 da aka sace tun 2025 a Filato

    January 10, 2026
  • Karin Wasu
    1. Kasuwanci
    2. Ilimi
    3. Nishadi
    4. Muhalli
    5. Lafiya
    6. Ra’ayi
    7. Wasanni
    8. View All

    Kamfanin Milo Ya Tallafa wa Masu Sana’ar Shayi 2,000 da Kayan Aiki a Kano da Jos

    August 23, 2026

    Gwamna Yusuf Ya Tallafa wa Matasa 1,116 Masu Tallace-Tallace da Masu Faci da Jarin Naira Dubu 50 Kowannensu

    July 23, 2026

    Yan Najeriya basa shayin kashe Kudi, sunyi amfani da Fetur na Naira Tiriliyan 1.58 a Bikin Kirsimeti -In Ji Gwamnatin Tinubu

    January 22, 2026

    Dangote ne ya rage farashin fetur da kaso 5.6%, shi ya sa farashi ya sauka ba saboda janye harajin 15% ba.

    November 19, 2025

    Masanin Kimiyyar Yanayi Daga Kano Dr. Salisu Ya Shiga Jerin Fitattun Masu Bincike na Duniya

    August 18, 2026

    Ya ce Yana Daukar Daliban A Matsayin ‘Ya ‘Yansa

    August 13, 2026

    Sabon Albashin Zai Fara Aiki A Watan Satumba

    August 10, 2026

    Na Amince Gwamna Yusuf Ya Kafa Tarihi a Bangaren Ilimi a Kano — In Ji Tsohon Kwamishinan Ilimi, Hon.Sunusi Kiru

    July 19, 2026

    An Amince da Fara Shirya Fim ɗin Maitatsine – Darakta

    January 9, 2026

    Karamin Yaron da Kakarsa Ta yi Sanadiyar Daukakarsa a Duniya ya Cika Shekara 12

    December 14, 2025

    MUTU KA RABA — HISBA ta ce aure tsakanin Mai Wushirya da ‘Yar Guda ba ta dauke shi da wasa ba

    October 21, 2025

    Majalisar Yara: Gwamna Yusuf ya baiwa yara aron zaman majalisar zartaswarsa a Kano dan girmama Ilimi

    January 13, 2025

    Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar cin tarar kuɗi ga duk wanda ya sake tofar da yawu ko majina akan hanya

    February 3, 2025

    Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta dauki sabbin matakan kare Muhalli

    January 31, 2025

    Daga yanzu an daina barin tilin shara akan titunan birnin Kano – Gwamnatin Kano

    January 13, 2025

    Gwamnan ya kai Ziyarar ne Cikin Dare.

    August 16, 2026

    Likitoci Su Daina Ƙaura Zuwa Ƙasashen Waje, Najeriya Na Buƙatar Su – Dr. Habib

    July 23, 2026

    Da ’Yan Najeriya Sun San Haɗarin Abincin da Ake Shanyawa a Gefen Hanya, Ko Kyauta Aka Ba Su Ba Za Su Ci Ba — Masana

    January 30, 2026

    WHO Ta Yi Kira Da A Kara Haraji Kan Barasa Da Abubuwan Sha Masu Dauke Da Sikari

    January 14, 2026

    “ADC Ba Ta Da Karfin Kuri’a a Kudu maso Yamma, Atiku Ya Kamata Ya San Da Haka” — Hon Shehu Isah

    August 16, 2026

    Ya kamata Hisba da Malamai a Kano su bayyana matsayinsu kan yadda yan siyasa ke jifan juna da kalmar LUWADI – Anas Hassan

    February 24, 2025

    Labarin dan Jaridar da ya kafa tarihi a duniyar yada labarai a kafar sadarwa ta zamani

    February 3, 2025

    Burinmu a yanzu shine Barau FC ta samu gurbin shiga gasar zakarun Nahiyar Africa – DSP Barau

    February 25, 2025

    An karrama jagoran kwallon kafa na Barau Jibiril Academy da lambar gwarzon shekara a bangaren Shugabanci

    December 21, 2024

    Kamfanin Milo Ya Tallafa wa Masu Sana’ar Shayi 2,000 da Kayan Aiki a Kano da Jos

    August 23, 2026

    Malaman Addinin Musulunci Daga Jihohin Arewa 19 Sun Goyi Bayan Tazarcen Tinubu A 2027

    August 23, 2026

    Hukumar Shari’a ta Kano Ta Wayar da Kan Jama’a Muhimmancin Kalandar Musulunci

    August 22, 2026

    Tinubu ya bada hutu Albarkacin ranar Haihuwar Annabi Muhammadu SAW

    August 21, 2026
TST HAUSATST HAUSA
Home » Kamfanin Milo Ya Tallafa wa Masu Sana’ar Shayi 2,000 da Kayan Aiki a Kano da Jos
Kasuwanci

Kamfanin Milo Ya Tallafa wa Masu Sana’ar Shayi 2,000 da Kayan Aiki a Kano da Jos

By tstAugust 23, 20263 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp
IMG 20260823 WA0111

Kamfanin Nestlé Milo ya tallafa wa matasa masu sana’ar sayar da shayi 2,000 a Kano da Jos, a wani shiri da aka ƙaddamar domin ƙarfafa ƙananan ‘yan kasuwa da kuma taimaka musu wajen bunƙasa sana’o’insu.

Tallafin ya ƙunshi kayayyakin aiki daban-daban da suka haɗa da risho mai amfani da iskar gas, tukunyar gas, malafar kare rana, fitila mai amfani da hasken rana, kofuna da kuma sinadarin Milo.

Kamfanin ya bayyana cewa shirin wani ɓangare ne na ƙoƙarinsa na ƙarfafa hulɗa da abokan cinikinsa tare da tallafa wa masu ƙananan sana’o’i, musamman masu sayar da shayi waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da karin kumallo ga jama’a a Arewacin Najeriya.

Da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar a Kano, wakilin Nestlé Milo a Najeriya, Gilbert Tweneboah-Koduah, ya ce tallafin ya nuna yadda kamfanin ke son ci gaba da kasancewa cikin al’umma tare da tallafa wa waɗanda ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum.

Ya ce masu sana’ar shayi sun zama wani muhimmin ɓangare na al’adar Arewacin Najeriya, inda mutane da dama ke dogaro da su wajen samun karin kumallo.

A cewarsa, shirin ya fara ne a bara da masu sana’ar shayi 400, amma yanzu an faɗaɗa shi zuwa masu sana’a 2,000 a Kano, Jos, Kaduna da Maiduguri, yayin da kamfanin ke shirin ƙara yaɗa shirin zuwa sauran sassan Arewacin Najeriya.

“Masu shayi sun zama wani muhimmin ɓangare na al’adar Arewacin Najeriya, inda jama’a da dama ke dogaro da su wajen karin kumallo”In ji shi

Milo na son kasancewa jigo a wannan al’ada tare da tallafa wa masu shayi domin su bunƙasa kasuwancinsu,” in ji shi.

Shugaban Ƙungiyar Masu Sayar da Shayi ta Jihar Kano, Usman Muhammad Usman, ya yaba wa Nestlé Milo bisa tallafin, yana mai cewa ya shafe shekaru 36 yana sana’ar shayi kuma Milo na daga cikin kayayyakin da ya daɗe yana hulɗa da su.

Ya ce kayan aikin da aka raba musu za su taimaka wajen sauƙaƙa harkokin sana’arsu da kuma ƙara inganta hidimar da suke yi wa kwastomominsu.

Shi ma wani mai sana’ar shayi a Jos, Musa Ibrahim, ya bayyana farin cikinsa da tallafin, yana mai cewa masu sana’ar shayi sun ji daɗin yadda kamfanin ya kula da su.

Ya kuma yi kira ga sauran kamfanonin da ke samar da kayayyakin da masu sana’ar shayi ke amfani da su da su yi koyi da Nestlé Milo wajen tallafa wa abokan hulɗarsu.

A nata jawabin, Jakadiyar Milo kuma fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Mansura Isa, ta ce kamfanin ya daɗe yana gudanar da ayyukan tallafa wa al’umma ta hanyoyi daban-daban.

Ita ma wani jakadan Milo kuma jarumin fina-finan Hausa, Sulaiman Yahaya, wanda aka fi sani da Bosho, ya jaddada muhimmancin amfani da albarkatun cikin gida wajen samar da kayayyakin kamfanin, yana mai cewa hakan na taimakawa wajen tallafa wa manoma da sauran masu ruwa da tsaki a cikin gida.

Nestlé Milo ya ce zai ci gaba da faɗaɗa shirin domin ƙarin masu sana’ar shayi a Arewacin Najeriya su samu kayan aikin da za su taimaka musu wajen bunƙasa sana’o’insu, inganta hidimarsu ga kwastomomi da kuma ƙara samun damar dogaro da kansu.

Share. Facebook Twitter Email Telegram WhatsApp

Related Posts

Gwamna Yusuf Ya Tallafa wa Matasa 1,116 Masu Tallace-Tallace da Masu Faci da Jarin Naira Dubu 50 Kowannensu

July 23, 2026

Yan Najeriya basa shayin kashe Kudi, sunyi amfani da Fetur na Naira Tiriliyan 1.58 a Bikin Kirsimeti -In Ji Gwamnatin Tinubu

January 22, 2026

Dangote ne ya rage farashin fetur da kaso 5.6%, shi ya sa farashi ya sauka ba saboda janye harajin 15% ba.

November 19, 2025

Dangote ya buɗe sabon kamfanin siminti mai darajar CEFA biliyan 100 a Côte d’Ivoire

October 13, 2025
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Kamfanin Milo Ya Tallafa wa Masu Sana’ar Shayi 2,000 da Kayan Aiki a Kano da Jos

August 23, 2026

Malaman Addinin Musulunci Daga Jihohin Arewa 19 Sun Goyi Bayan Tazarcen Tinubu A 2027

August 23, 2026

Hukumar Shari’a ta Kano Ta Wayar da Kan Jama’a Muhimmancin Kalandar Musulunci

August 22, 2026

Tinubu ya bada hutu Albarkacin ranar Haihuwar Annabi Muhammadu SAW

August 21, 2026

Masanin Kimiyyar Yanayi Daga Kano Dr. Salisu Ya Shiga Jerin Fitattun Masu Bincike na Duniya

August 18, 2026
Advertisement
© 2026 TST HAUSA Developed by ENGRMKS & CO..
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.