Hukumar HISBA ta Jihar Kano ta yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa shahararren matashin TikTok, Idris Mai Wushirya, zai iya sakin Basira Yar Guda kwana ɗaya bayan daura aurensu
Mataimakin kwamadan hisba a bangaren ayyuka na musamman Dr. Mujahedeen Aminuddeen Abubakar, shine ya shaida hakan a zantawarsa da Rahma Radio,Kano a Safiyar Talata.
Yace sun karbi umarnin kotun Magestry na daura auren mutanan biyu bayan wani bidiyo da suka fitar na badala da nufin samun magoya baya a shafukan sada zumunta na zamani.
Yace tuni shirye shirye suka kammala shiri na daura auren cikin shirin kuwa harda fara binciken iyayansu da magabata da kuma koshin lafiyarsu.
Hisba din ta kuma yi gargadin cewa koda mutanan biyu sunyi niyar kwatar kansu daga kotu domin samun sauki wanda shine yasa suka fake da cewa suna kaunar junansu a gaban kotu,to su sani cewa wannan aure mutu ka raba kuma hukumar bata dauki maganar da wasa ba,kamar yadda Dr Mujahideen Aminudden ya shaida.
Yace auren Yana karkashin kulawar Hisba ko bayan an fara zaman auren.
Hukumar ta kuma shawarci ma’auratan da su yi auren su da niyyar gina gida mai tsari da natsuwa, ba don neman farin jini ko shahara a kafafen sada zumunta ba.
Daga nan Dr. Muhajedden ya gargadi matasa da su guji neman magoya baya ta kowacce hanayaa shafukan sada zumunta na zamani,domin hakan watarana zai kai mutum ga halaka.
TST Hausa ta rawaito cewa Hisba ta ƙara jaddada cewa za ta ci gaba da sa ido domin tabbatar da duk wani aure da ake yi a cikin jihar yana bin ƙa’idojin addini da dokokin ƙasa.

