Shugaban hukumar kula da Alhazan Najeriya NAHCON Ambassada Isma’ila Abba Yusuf ne ya tabbatar da hakan lokacin da tawagar hukumar Alhazan Kano suka kai masa ziyara a Ofishin hukumar dake birnin Makka.
Tawagar hukumar Alhazan Kano sunje ne karkashin Jagorancin Amirul Hajj na Kano kuma sarkin Gaya Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya da shugaban hukumar a Kano Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle.
TST Hausa ta rawaito Wakilinmu cewa tawagar hukumar Alhazan ta Kano ta kai ziyara Ofishin hukumar Alhazan Najeriya a Makka ne domin tabbatar da samun jadawalin fara dawo da Alhazan Kano gida.
Saidai a zantarawarsa da manema labarai Ambassada Isma’ila yace NAHCON bata kaunar ta ga wani Alhajinta ya shiga damuwa kafin da bayan kammala aikin Hajj.
Dan haka yace da yiyuwar cikawa Alhazan da suka kosa da Zaman Makka ko Guzurinsu ya Kare a dawo da su a sahun Farko zuwa Kano.

