Jami’an tsaro na Farin Kaya DSS a Jihar Kano sun kama wani matashi mai Suna Aminu Muktar da ake zargi da sace wani ƙaramin yaro mai shekara uku a ƙaramar hukumar Minjibir.
TST Hausa ta rawaito cewa wanda ake zargin dan asalin garin Minjibir ya nemi Naira miliyan 15 a matsayin kuɗin fansa daga hannun mahaifin yaron kafin a sake shi.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ina-rokon-dss-da-ofishin-nsa-su-binciki-masu-cewa-na-mutu-akpabio/
Sai dai kafin ya samu nasarar karɓar kuɗin, jami’an tsarona DSS suka cafke shi tare da ceto yaron.
An kama matashin ne a garin Jogana dage Gezawa.
A yayin bincike, matashin ya bayyana cewa ya samu tunanin aikata laifin ne bayan kallon wani fim da ke nuna yadda ake sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Rahotanni sun ce yaron na cikin koshin lafiya bayan ceto shi,kuma tuni DSS a Kano suka mikashi wajen mahaifinsa yayin da jami’an ke ci gaba da bincike domin gano ko akwai wasu da ke da hannu a lamarin.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ina-rokon-dss-da-ofishin-nsa-su-binciki-masu-cewa-na-mutu-akpabio-2/
Hukumomin tsaro irin na DSS sun jaddada cewa za su ci gaba da tsaurara matakan tsaro domin dakile ayyukan masu satar mutane da ke barazana ga zaman lafiyar al’umma.
Ana sa ran za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

