Dr. Salisu Lawal Halliru, malami a Jami’ar Ilimin gwamnatin tarayya ta Yusuf Maitama Sule dake birnin Kano wato Federal University of Education Kano, na daga cikin ƙwararrun masana kimiyyar sauyin yanayi guda takwas da aka zaɓa a Najeriya a matsayin wadanda zasu halarci babban taro a birnin Bahamas dake kasar Caribbean.
Zaɓen Dr. Salisu nasa ya shafi irin kwazonsa a bangaren bincike da kwarewa a ilimim sauyin yanayi.
Taron na kasar Caribbean zai mayar da hankali kan tasirin sauyin yanayi a duniya karkashin kulawar babbar cibiyar dake nazari da bincike akan sauyin yanayi ta majalisar dinkin duniya.
Rahotanni na cewa Dr. Salisu Lawal zai gabatar da mukala akan sauyin yanayi da yadda ake fuskantar kalubalen, da hanyoyin daidaita rayuwa da sauyin yanayi.
A cewar sanarwar da babbar ciniyar ta sauyin yanayi wato IPCC ta fitar,tace ana sa ran Dr. Halliru da sauran masana za su halarci taron karo na biyu da za a gudanar a Bahamas, a farkon watan Mayun 2026.
Rahoton ya bayyana cewa taron LAM2 na da matuƙar muhimmanci wajen ci gaba da aikin shirya rahoton maganance matsalar yanayi a duniya.
Babbar cibiyar ta IPCC na ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin duniya da ke tattara bayanai da nazari kan sauyin yanayi, inda rahotanninta ke taimakawa gwamnatoci da masu yanke shawara wajen ɗaukar matakan da suka dace kan matsalolin sauyin yanayi.

