Wani babban taron tattaunawa kan jagoranci da aka gudanar a birnin London na ƙasar Birtaniya, a ranar Alhamis 4 ga Fabrairu, 2026, ya ba marubuciya kuma ƙwararriyar mai horaswa kan jagoranci daga Najeriya, Dr Asma’u Isah Maibasira, damar kaddamar da sabon littafinta mai taken Facilitator’s Edge: A Guide for Expert Learning Design and Techniques a gaban mahalarta daga sassa daban-daban na duniya.
Taron, wanda aka shirya a matakin ƙasa da ƙasa ƙarƙashin taken “Kallon Gaba: Dabarun Jagoranci a Tattalin Arzikin Ilimi,” ya haɗa malamai, masu tsara manufofi, ‘yan kasuwa da ƙwararru a fannin ilmantarwa, domin tattauna sabbin buƙatu da ƙalubalen jagoranci da yada ilimi a duniyar da ke ci gaba da sauyawa.
Kaddamar da littafin Facilitator’s Edge ta kasance ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka fi jan hankali a taron, inda aka mayar da hankali kan jagoranci na zamani, ingantacciyar horaswa da sabbin dabarun tsara ilmantarwa.
Mahalarta sun tattauna hanyoyin da shugabanni da masu horaswa za su dace da tattalin arzikin da ya dogara da ilimi, wanda ke buƙatar haɗin kai, tunani mai zurfi da ilmantarwa ta aikace.
Dr Maibasira, wadda ke da digirin digirgir (PhD) kuma ta fito daga Arewacin Najeriya, ta shahara wajen ayyukanta a fannin bunƙasa jagoranci, horaswa da tsara ilmantarwa.
Duk da ayyukanta a ƙasashen waje, tana ci gaba da taka muhimmiyar rawa a gida ta hanyar ba da jagoranci da shawarwari ga matasa masu kasuwanci, musamman mata.
Da take jawabi a taron, marubuciyar ta bayyana cewa littafin Facilitator’s Edge amsa ce ga gibin da ke ƙaruwa tsakanin isar da ilimi da cimma sakamakon ilmantarwa mai amfani. Ta jaddada cewa ingantacciyar horaswa ba wai wuce bayanai kaɗai ba ce, sai dai taimaka wa masu koyo su fahimta da amfani da ilimi a aikace.
Taron ya ƙunshi tattaunawa ta musamman wadda Chris Bishop, wanda ya kafa mujallar Forbes Africa, ya jagoranta, tare da zaman kwamitin masana da suka haɗa da ƙwararru a fannin jagoranci, manufofi da fasaha.
An kaddamar da littafin a gaban manyan baki daga Najeriya da ƙasashen waje, ciki har da Babban Jakadan Najeriya a Birtaniya, Ambasada Maina Maidugu, wanda aka wakilta a taron.
Sauran manyan baki sun haɗa da DCG Isah Umar Gusau (Rtd) na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Hajiya Kikelomo Adewale Adeniyi, Shugabar Ƙungiyar Matan Jami’an Kwastam ta Ƙasa, da Dr Ken Giami, mawallafin African Leadership Magazine, da sauran fitattun baki.
Littafin Facilitator’s Edge shi ne na uku da Dr Maibasira ta wallafa, bayan Business Geek da tsohon sigar Facilitator’s Edge, waɗanda suka samu karɓuwa sosai a tsakanin masu horaswa da ƙwararru a Afirka da ma wajen Afirka. Ayyukanta na ci gaba da mayar da hankali kan bunƙasa jagoranci, tsara ilmantarwa da ba da jagoranci ga matasa masu tasowa.

