An shirya gangamin taron murnar cika shekaru 30 da kafuwar Cibiyar addinin Musulunci ta Usman bn Affan Gadon Kaya a Kano, taron da daraktan cibiyar Dr. Aliyu Yunus da Dr. Abdullahi Usman Gadon Kaya suka jagoranta, inda malamai,da dalibai da manyan baki daga sassa daban-daban suka hallara.
Cibiyar, wacce marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam (Allah ya jikansa) ya assasa a shekarar 1996, ta shafe tsawon lokaci tana bayar da gagarumar gudunmawa wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci, da tarbiyyar al’umma bisa tafarkin Ahlus Sunnah.
A yayin taron, daraktan cibiyar Dr. Aliyu Yunus ya godewa Allah da dukkanin wadanda suka bada gudun mawa wajen cigaban cibiyar.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/hudubasalon-sunan-gwamnatin-tinubu-na-muslim-muslim-bai-amfanar-da-musulmai-ba-sai-cutar-da-su-dr-aliyu-yunus/
Yace cibiyar ta yi fice wajen yaye dubban dalibai da malamai, waɗanda a yau ke taka muhimmiyar rawa a fannonin koyarwa,da wa’azi da jagorancin addini a sassa daban-daban na jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.
Daga nan yace a yanzu shiri yayi nisa wajen dora cibiyar akan tafarkin koyarwa daidai da zamani.
A nasa jawabin Limamin Masallacin juma’a na Usman bn Affan Gadon Dr.Abdallah Usman Gadon kaya wanda yana daga cikin fitattun waɗanda suka kammala karatu a cibiyar har ya kawo wannan matsayi yace cibiyar ta yaye Dalibai masu tarin yawa a fannoni daban daban ciki harda manyan likitoci da masu tuka jirgin sama.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/huduba-masu-yada-jita-jita-na-daga-cikin-wadanda-suka-hana-najeriya-zama-lafiya-farfesa-rijiyar-lemo/
Bugu da ƙari, cibiyar ta assasa Masallacin Usman bn Affan Gadon Kaya, wanda ya zamo cibiyar ibada, koyarwa da shiryarwa, tare da ƙarfafa haɗin kai da fahimtar addini a tsakanin al’umma.
TST Hausa ta rawaito cewa cibiyar wacce aka kafa a shekarar 1996 tun bayan kafuwarta, cibiyar ke ci gaba da bunƙasa harkokin ilimi da wa’azi, tare da samar da malamai masu ingantaccen ilimi da tarbiyya, waɗanda ke ba da gudunmawa wajen gyaran al’umma da bunƙasa zaman lafiya.
Masu halartar taron irinsu sheikh Malam Ibrahim Khalil sun yaba da jajircewar shugabannin cibiyar tare da kira ga al’umma da masu hannu da shuni da su ci gaba da tallafa wa cibiyar, domin ta ci gaba da rawar da take takawa wajen gina al’umma bisa ilimi da addini.

