Rukunin Kamfanonin Dangote ya kaddamar da aikin gina kamfanin takin zamani mai suna Dangote Gode Fertiliser Plant a garin Gode, ƙasar Habasha.
Shugaban rukunin, Alhaji Aliko Dangote, shi ne ya jagoranci bikin kaddamarwar, wanda ya ja hankalin manyan jami’ai da masu ruwa da tsaki a harkar tattalin arziki.
Cikin fitattun baƙin da suka halarci taron akwai Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, shugaban Kamfanin MRS, Sayyu Dantata, shugaban rukunin kamfanonin NGX, Umaru Kwairanga, da kuma shugaban kamfanin hannun jari na Habasha, Biru Taye.

