Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin bincikar ɗan majalisar da ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Nasarawa, MB Aliyu, bayan an shigar da ƙorafi a kansa kan zargin aikata abin da ya saɓa wa ɗa’ar majalisa dangane da Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma cin zarafin Zomo.
Ɗan majalisar da ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Minjibir, A.A. Minjibir, ne ya gabatar da ƙorafin, inda ya danganta shi da wani faifan bidiyo da ake zargin ya nuna MB Aliyu yana jan kunnen zomo, lamarin da ya ce bai dace da ɗabi’a da ƙa’idojin majalisar ba.
A yayin gabatar da ƙorafin, A.A. Minjibir ya bayyana cewa abin da ake zargin ɗan majalisar ya aikata ya saɓa wa ƙa’idojin da ake buƙatar mambobin majalisar su kiyaye wajen gudanar da ayyukansu.
Shi ma ɗan majalisar Kumbotso, Hon. Muddassir Zawaciki, ya goyi bayan ƙorafin, inda ya bayyana cewa za su gana da MB Aliyu domin jin ta bakinsa kan zargin da ake yi masa.
Ana sa ran majalisar za ta saurari bayanin ɗan majalisar tare da nazarin ƙorafin kafin yanke shawarar matakin da ya dace, bisa tanade-tanaden dokokinta.
Sai dai, har yanzu batun yana matsayin zargi, kuma ana buƙatar jin bayanin MB Aliyu kafin a cimma matsaya kan lamarin.

