Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana fatanta na barin fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock a shekarar 2031, inda take fatan shiga Najeriya da za ta ba ta damar more rayuwa cikin kwanciyar hankali.
Oluremi Tinubu ta bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da hedikwatar ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement a Abuja, wadda ke gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a da neman goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.
Ta ce burinta shi ne ta ga an samu ci gaban da zai sa ’yan Najeriya su more rayuwa, har da ita kanta, lokacin da za ta bar fadar shugaban ƙasa a shekarar 2031.
A kalamanta, ta ce: “Ina son barin Aso Rock amma sai a shekarar 2031, da yardar Allah, in shiga Najeriya da ni kaina, a matsayina na mace mai shekaru sama da 70, zan ji daɗin rayuwa a cikinta.”
Uwargidan shugaban ƙasar ta kuma bayyana sauye-sauyen da ake samu a filayen jiragen sama a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da take ganin suna nuna ci gaba a Najeriya.
Ta ce tana fatan samun sauƙin tafiye-tafiye, musamman wajen zuwa filayen jiragen sama da kuma yin zirga-zirga cikin sauri da sauƙi.
A yayin taron, Oluremi Tinubu ta ƙaddamar da hedikwatar ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement a Abuja, tare da bayyana aniyar ƙungiyar na tallafa wa nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen shekarar 2027.
Ta kuma bayyana goyon bayanta ga jam’iyyar APC da kuma jagoran ƙungiyar, Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo.
Tun kafin Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban ƙasa, Oluremi ta kasance tana bayyana goyon bayanta ga manufofinsa tare da nuna kwarin gwiwarta kan yadda zai tafiyar da mulki.
A watan Oktoban 2022, lokacin da Tinubu ke neman shugabancin Najeriya, ta bayyana cewa ƙwarewar da ya samu a matsayinsa na tsohon gwamnan Legas za ta taimaka masa wajen magance matsalolin ƙasar.
Bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, ta riƙa kira ga ’yan Najeriya da su yi haƙuri, tana mai cewa ba za a iya magance matsalolin ƙasar cikin dare ɗaya ba.
Haka kuma, a wani taron addu’ar bikin samun ’yancin kai a watan Oktoban 2023, ta bayyana cewa gwamnatin mijinta ta gaji matsalolin da suka daɗe suna addabar ƙasar, kuma tana ƙoƙarin magance su maimakon ɗora alhakin matsalolin kan gwamnatocin baya.

