Limamin Masallacin Gadon Kaya da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano, Dr. Abdullah Gadon Kaya, ya yi kira ga iyaye da su kara mayar da hankali wajen kula da tarbiyar ’ya’yansu tun suna kanana.
Dr. Gadon Kaya ya yi wannan gargadin ne a cikin hudubar Juma’a mai taken “Kula da Tarbiyar Yara tun suna Kanana”, inda ya jaddada muhimmancin bai wa yara isasshen lokaci da kulawa domin tabbatar da kyakkyawar tarbiyyarsu.
Malamin ya ce rashin samun lokacin zama da yara, musamman daga iyaye masu yawan shagaltuwa da sana’o’i, na daga cikin abubuwan da ke iya haifar da matsalolin tarbiyya a tsakanin yara.
Ya gargadi iyaye, musamman ’yan kasuwa, da cewa kada neman abin duniya ya sa su yi sakaci da hakkokin ’ya’yansu, yana mai cewa Allah zai tambayi iyaye kan yadda suka kula da tarbiyar ’ya’yansu da lokacin da suka ba su.
Dr. Gadon Kaya ya kuma ja hankalin iyaye kan muhimmancin kula da abincin da suke bai wa ’ya’yansu, da kuma tabbatar da cewa abin da suke ci da yadda suke rayuwa ya dace da koyarwar addini da kyawawan dabi’u.
Ya bukaci iyaye su dora ’ya’yansu kan kyawawan halaye tun suna kanana, tare da koyar da su girmama na gaba da su, biyayya ga iyaye da manya, da kuma mutunta sauran al’umma.
Haka kuma, ya yi kira ga iyaye mata da su kara fahimtar dabi’u da halayen ’ya’yansu, domin su iya gano sauye-sauyen da ka iya nuna cewa yaro yana fuskantar wata matsala ko kuma yana shiga cikin dabi’un da ba su dace ba.
Malamin ya ce tarbiyar yara ba nauyin uwa ko uba kadai ba ce, illa dai nauyi ne da ya rataya a wuyan iyaye baki daya, domin kyakkyawar tarbiyya ita ce ginshikin samar da al’umma mai nagarta.
Ya kuma bukaci iyaye da su rika zama abokai ga ’ya’yansu, su saurare su, su san irin mutanen da suke mu’amala da su da kuma abubuwan da suke kallo ko koya, musamman a wannan zamani na kafafen sada zumunta.
Dr. Abdullah Gadon Kaya ya ce kula da yara tun suna kanana na taimakawa wajen hana su fadawa cikin munanan dabi’u da matsalolin da kan iya shafar rayuwarsu da makomarsu.

