Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya ta duba yiwuwar dakatar da yakin neman zabe a wasu jihohin Arewa guda takwas, sakamakon tabarbarewar tsaro.
Dan Majalisar dattawa daga jihar Bauchi Sanata Abdul Ningi,ne ya gabatar da bukatar hakan wanda ya bayyana damuwa kan karuwar hare-haren ‘yan ta’adda da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.
A cewarsa, bai kamata a ci gaba da harkokin siyasa ba a daidai lokacin da jama’a ke fuskantar barazanar tsaro, yana mai cewa wajibi ne a fifita kare rayuka kafin komai.
Jihohin da aka ambata sun hada da Borno,da Plateau, da Bauchi,da Benue,da Niger,da Sokoto, da Kebbi da wasu sassan Kano, inda ake ci gaba da samun hare-hare.
Majalisar ta kuma bukaci hukumomin tsaro su kara kaimi wajen shawo kan matsalar, tare da kubutar da mutanen da ke hannun ‘yan bindiga, musamman a yankunan da abin ya fi kamari.
Wannan mataki na zuwa ne a lokacin da ake ganin siyasar zaben 2027 na kara karfi, duk da matsalolin tsaro da ke addabar wasu sassan kasar nan.
Ya ce kuskure ne a tafi yakin neman zaben 2027 alhalin mutane na fama da matsalar tsaro

