Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya bayyana matsayinsa kan al’amuran siyasa da ke gudana a yankinsa, inda ya nuna kwarin gwiwa da jajircewa kan abin da ya shafi tafiyarsa ta siyasa.
Sanata Kawu Sumaila, ya ce duk ɗan siyasar da ya sanya bunƙasa harkar ilimi a gabansa, zai fuskanci ƙalubale matuƙa, kasancewar da yawa daga cikin ƴan siyasa sun fi son harkar da za’a buga a kwashe lokaci guda.
Kawu ya yi wannam gugar zana ne a jami’ar Aliko Dangote dake Wudil a lokacin da yake bajekolin ayyukan da ya gabatar a ɓangaren ilimi musamman ɗaukar nauyin ɗalibai sama da 100 domin cigaba da karatu a matakai daban-daban.
A cikin kalaman da ya yi Kawu Sumalai ya gode wa Allah kan dukkanin yanayin da ake ciki, yana mai nuna cewa idan wannan shi ne mafi alkhairi, wato ya yi Falle daya to Allah yasa shine mafi alkairi sanann ya karɓi gaddara da godiya.
Kawu Sumaila ya jaddada cewa ba yatsoron kowa, tare da nuna cewa duk wanda ke ganin yana da iko a kan rayuwarsu, ya gwada hakan a aikace.
Dan majalisar na wannan martanin ne kwana daya bayan shutabanin Kananan Hukumomin Kano ta kudu sun nuna goyon bayansu ga neman Hon Allasan Rurum ya maye gurbinsa a majalisar Dattawa.

