Rahotanni da ke fitowa sun nuna cewa shugabannin kananan hukumomi 16 na shiyyar Kano ta Kudu sun bayyana goyon bayansu ga Hon. Kabiru Alhassan Rurum domin maye gurbin Abdurahaman Kawu Sumaila a takarar kujerar Sanatan Kano ta Kudu a zaben shekarar 2027.
Anyi zaman ne karkashin jagorancin shugabar karamar hukumar Tudun Wada kuma Algon ta shugabannin Kananan Hukumomin Kano, Hajiya Sa’adatu matar Soja.
Rahotanni nacewa wannan matsaya ta fito ne bayan wani muhimmin taro da shugabannin suka gudanar, inda suka tattauna halin da yankin ke ciki da kuma bukatar samun wakilci nagari a matakin majalisar dattawa.
A cewar rahoton, shugabannin sun jaddada cewa sun cimma matsayar ne bisa la’akari da kwarewa da gogewar Rurum, tare da ganin shi ne ya fi dacewa da wakiltar muradun al’ummar Kano ta Kudu.
Sai dai har zuwa yanzu, ana sa ran karin bayani daga bangaren Rurum da kuma yiwuwar fitowar sauran ‘yan takara.
Har zuwa yanzu Kabiru Rurum bai ce komai ba game da tayin.
A shekarar 2023 ne Sanata Kawu Sumaila ya kayar da Sanata Kabiru Gaya a jam’iyar NNPP.

