Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na Asabar din karshen wata da aka saba gudanarwa a duk fadin jihar, sakamakon ziyarar aiki da mai ɗakin shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu,ta kawo jihar.
Rahotanni sun nuna cewa tuni mai dakin shugaban kasa Remi Tinubu ta koma Abuja daga Kano, a yammacin Alhamis.
Saidai a a cikin wata sanarwa da Daraktar wayar da kan jama’a ta ma’aikatar Muhalli da sauyin yanayi ta jihar Kano Hajiya Maryam Abdulkadir ta fitar ta ce an dauki matakin dakatar da tsaftace muhalli ne domin bai wa mahalarta taron kwana uku da aka kaddamar na bunkasa sana’oi na shiyar Arewa maso yamma dake gudana a kano cikakkiyar kulawa, tare da tabbatar da tsaro da kuma sauƙaƙa zirga-zirga a jihar.
Sanarwar ta ƙara da cewa dakatarwar ba zata hana jama’a kulawa da tsaftace muhallansu ba lungu da sako.
Sanarwar ta ce aikin tsaftar ofisoshin gwamnati da ma’aikatu da tashoshin mota da kasuwanni da aka saba gudanarwa duk ranar juma’a ta karshen wata na nan daram.
Uluremi wacce ta kaddamar da bude taron bunkasa tattalin arziki da karfafa sana’o’i, musamman ga mata da matasa a jihar Kano ana sa ran zai kawo sauyi a Arewa maso yammacin Najeriya.

