Jigo a APCn Kano kuma fitaccen ɗan siyasa a Jihar , Shehu Isa Driver, ya bayyana shakkunsa kan dawowar Hon. Kabiru Alhassan Rurum zuwa jam’iyyar APC, yana mai cewa akwai tambayoyi kan ainihin manufar komawar tasa.
Hon. Driver ya ce wasu alamomi na nuni da cewa matakin na iya kasancewa yana da nasaba da shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen 2027.
Ya kara da cewa, a baya an yi ta rade-radin cewa Rurum na zawarcin kujerar mataimakin gwamnan Kano, yayin da a halin yanzu kuma ake alakanta sunansa da yiwuwar tsayawa takarar Sanatan Kano ta Kudu, wanda hakan ka iya kawo rigingimu a siyasar kano da yankinsa.
A cewarsa, wannan ne ya janyo wasu ‘yan jam’iyya ke nuna shakku kan ko dawowar Rurum APC ta fito ne daga zuciya ɗaya domin haɗa kan jam’iyyar, ko kuma wata dabara ce ta cimma burin siyasa a nan gaba.
Watakila anan gaba magoya bayan Rurum ko shi kansa su baiwa Shehu Isa Direba amsa

