Ministan Wutar Lantarki na Najeriya, Adebayo Adelabu, ya yi murabus daga mukaminsa domin mayar da hankali kan takarar gwamnan Jihar Oyo a zaben 2027.
A cikin wasikar da ya aikawa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, Adelabu ya bayyana cewa murabus dinsa zai fara aiki ne daga ranar 30 ga watan Afrilu, 2026, domin ba da damar mika ragamar aiki cikin tsari.
Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki ya yi daidai da dokokin zabe na Najeriya, wadanda ke wajabta wa masu rike da mukaman gwamnati sauka kafin su shiga takara.
Adelabu ya gode wa Shugaban Kasa bisa damar da aka ba shi ya yi hidima, yana mai cewa zai ci gaba da bayar da gudunmawa ga cigaban kasa ta wata hanya.
Murabus dinsa na zuwa ne a daidai lokacin da ake fara dumamar siyasar zaben 2027, musamman a Jihar Oyo inda ake sa ran fafatawa mai zafi.

