Babban kwamandan hukumar Hisba ta jihar Kano Shiek Aminu Ibrahim Daurawa ya ce ,samar da hukumomin Hisba a jihohin Arewa zai taimaka wajen magance aikata bada a yankin.
Kwamandan na Hisba a kano ya shaida hakan ne bayan kammala ziyarar zuwa jihohin Yobe da Bauchi da Sokoto a kokarin da jihohin sukeyi na samar da hukumomin Hisba kamar yadda Kano ta samar da hukumar a shekarar 2003 zamanin tsohon gwamnan kano Rabiu Musa kwankwaso.
A shekarar 2005 ne Kuma zamanin tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya mayar da ayyukan hukumar doka a shekarar 2005 a majalisar dokokin kano.
Jihohin uku sunga dacewar samar da hukumar ta Hisba ne domin magance matsalolin zamantakewar jama’a da ayyukan da suka saba da al’adun jama’a.
TST Hausa ta rawaito cewa gwamnonin jihohin Yobe da Sokoto da Bauchi ne suka nemi shawarwarin kwamandan hukumar hisa ta Kano kafin kaddamar da hukumar a jihohinsu.
A yayinda yake Karin haske,bayan kammala ziyara jihohin uku, Shiek Daurawa ya ce hatta ragaita almajirai da mata masu zaman kansu hukumomin hisbar zasu hada karfi domin magance wannan matsalar.
Rahotanni nacewa , gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nuna farin cikinsa abisa wannan yunkuri da jihohin uku sukayi na koyi da hukumar Hisba ta Kano.
Wata majiya ta shaida cewa ,wannan yunkurin yasa gwamnatin kano ta dauki nauyin baiwa sabbin jami’an hukumar hisba ta jihohin Yobe da Sokoto da Bauchi da Shugabanninsu horo na musamman domin sanin makamar aiki.
Taron bitar zai fara gudana ne a Kano daga ranar Juma’a 3 ga watan Janairun 2025.
Ana sa ran farawa da sabbin jami’an hukumar hisba ta jihar Yobe a ranar Juma’a zuwa Lahdi

