Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Muhammad Saad Abubakar ya nuna matukar damuwarsa a kan yadda bangaren shari’a ya taɓarɓare, ta yadda masu kuɗi kawai ke samun galaba a kotu.
Abubakar wanda ya gabatar da wannan jawabi ne a taron ƙungiyar lauyoyin Najeriya da ya gudana a birnin Enugu, inda ya ce shari’a a Najeriya na neman komawa ‘dai dai kuɗin ka, dai dai shagalin ka’, inda masu hannu da shuni ke saye alkalai domin samun nasara, yayin da talakawa kuwa ke asarar haƙƙoƙin su.
Sarkin Musulmin ya ce wannan ta sa masu hannu da shuni ke aikata laifuffukan da suka ga dama ba tare da wata fargaba ba, saboda sun san babu abinda zai faru.
Abubakar ya bayyana bacin ransa da yadda kima da mutuncin alkalai ke ci gaba da zubewa, inda ya buƙaci taron lauyoyin, waɗanda ya bayyana su a matsayin masu matuƙar muhimmanci a bangaren shari’a, da su ɗauki matakan gyara domin ceto wannan bangare mai matukar muhimmanci, ganin yadda cin hanci da rashawa da nuna fifiko ga wani bangare ke neman durƙusar da shi.
Sarkin Musulmin ya buƙaci lauyoyin da su dawo da kimar bangaren shari’a wajen kare dokokin ƙasa da kuma tabbatar da gaskiya da kuma adalci a tsakanin al’umma, ba tare da nuna banbanci tsakanin masu hannu da shuni da kuma talakawa ba.
Abubakar ya buƙaci ganin shari’a tayi aikin ta a kan kowanne ɗan Najeriya, ba tare da bai wa masu kuɗi ko kuma masu rike da muƙaman gwamnati gaskiya ko da kuwa su ne masu laifi ba.
Sarkin Musulmin ya buƙaci lauyoyin da su yi amfani da taron su wajen tattauna manyan kalubalen da suka shafi bangaren shari’a da zummar ganin sun samo mashalar da za ta inganta aikin da su ke yi.
Abubakar ya ce ƴan Najeriya da dama na sanya ido a kan lauyoyin da kuma ayyukan da suke yi, kuma su kaɗai za su samarwa kan su kima, wajen tabbatar da ganin doka da oda ta yi aikin ta, ba tare da fifita wani bangare ko kuma bai wa wani bangare damar cin karen sa babu babbaka ba.
Sarkin Musulmin ya ce yin haka zai dawo da kimar aikin a idan jama’a, da kuma kawo karshen matsalar shugabancin da ta addabi Najeriya.

