Rahotanni daga sassan Najeriya sun nuna cewa farashin kwai ya fara sauka a kasuwanni, bayan wani lokaci da aka shafe ana fuskantar hauhawarsa.
A wasu yankuna, ana samun raguwar farashin kwai daga kimanin N3,500 zuwa N2,800 kiret daya mai ɗauke da kusan ƙwai 30.
Masana harkar noma da kasuwanci sun danganta wannan saukar farashin da karuwar samar da kwai daga gonakin kaji, da kuma sauyin yanayi da ya taimaka wajen rage asarar kaji da kwai.
Sauran dalilai sun haɗa da ƙoƙarin gwamnati wajen tallafa wa manoman kaji da kuma rage farashin abincin kaji kamar masara da sauran kayan abincinsu.
TST Hausa ta rawaito cewa farashin masara daya daga cikin manyan sinadaran abincin kaji yanzu ya ragu da kaso 33 cikin 100 inda buhun ton daya ake sayarwa a kan Naira 450,000, idan aka kwatanta da Naira 600,000 a farkon shekarar nan.
Shugaban Kungiyar Masu Kiwo Kaji ta Najeriya (Poultry Association of Nigeria “PAN”), Sunday Ezeobiora, ya bayyana cewa saukar farashin masara da wake ya ba masu kiwo damar rage farashin samar da kwai, wanda hakan ya haifar da rage farashin kwai ga masu saye.
Ya umarci duk masu sayar da kwan kaji su sauke farashinsa.
Sai dai wasu ‘yan kasuwa sun bayyana cewa har yanzu akwai yankuna da farashin bai canza ba, musamman a wuraren da ake fama da tsadar sufuri ko karancin kayayyaki.
Ana sa ran saukar farashin zai ba wa talakawa damar cin gajiyar ingantaccen abinci a farashi mai sauƙi, musamman a wannan lokaci da ake fama da tsadar rayuwa.

