Tsohon Shugaban jam’iyar ANP ta Najeriya wato Alliance National party Hon.Shittu Mashood da kafi sani da Asuwaju ya nemi dan takarar Shugabancin Najeriya a zaben 2023 Sanata Rabiu Musa kwankwaso da kada yayi gaggawar hadewa da wata jam’iyya a yanzu.
Mashood ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a fadar gwamnatin Kano.
Yace lokacin hadewa da wata jam’iyya baiyi ba tukunna.
Hon.Shittu Mashood wanda makusancin sanata Rabiu Musa kwankwaso ne yace saboda gudun yaudara yasa basa goyon bayan Kwankwaso ya mika wuya ga wata jam’iyya a yanzu.
Yace a shekarar 2023 ya na daga cikin na gaba gaba wajen ganin anyi hadaka domin kayar da jam’iyar APC,kuma anyi nasara,tunda jam’iyar dakyar takai ban tanta.
Ya kara dacewa suna sane da masu korafe korafen cewa Sanata Rabiu Musa kwankwaso yaki nuna alkibilarsa ta siyasa,yana mai cewa shuru din da yayi,shima siyasa ce.
“Babu wani mutum da a yanzu Kwankwaso zaibi a tafiyar siyasa a gabanin zaben 2027, saboda yawancin masu son Kwankwaso ya mika musu wuya ,ba Najeriya ce a gabansu ba”;Inji Shittu.
Yace masu sukar madugun kwankwansiyya cewar bashida wani katabus a siyasar Najeriya kuma bashi da iko da ya wuce Kano,Hon Shittu yace masu irin wannan magana ba komai sukayi ba sai karawa Kwankwaso farin jini.
TST Hausa ta rawaito cewa,a yayin taron manema labarai din ,Hon Shittu ya bayyana rawar da Kwankwaso ya taka wajen samun nasarar APC gabanin zaben 2015 ,Inda yace a hadakar zaben 2023 wasu ne suka zo da son zuciya shiyasa ba’a samu nasara ba yadda ya kamata.
Daga karshe yace akwai sauran lokaci,da anan gaba a cikinsa ne Kwankwaso zaiyi nazarin makomar siyasarsa a Najeriya.

