Rage Farashin Fetur da mukayi shine dalilin sauke farashin a Najeriya ba janye Harajin kaso 15 ba – Matatar Dangote
Matatar man fetur ta Dangote Refinery ta karyata rahotannin da suka bayyana cewa saukar farashin man fetur a kasuwanni shi ne yasa gwamnatin tarayya ta janye harajin shigar da man fetur na kaso 15 cikin 100.
A sanarwar da matatar ta fitar, tace janye harajin bashida alaka da janye Harajin da gwamnatin tarayya ta yi.
Matatar tace raguwar farashin litar man da aka gani ya samo asali ne bayan da matatar ta rage farashin daga naira 877 zuwa naira 828 a kowace lita tun a ranar 6 ga Nuwamba.
Wani Labarin: Yakin Iran da Isra’ila: NNPC ya kara litar man fetur a Kano da sauran jihohin Najeriya
Matatar tace duk da cewa wasu kafafen yada labarai sun danganta saukar farashin da janye haraji, babu gaskiya a cikin wannan zargin domin harajin shigo da kaya har yanzu yana nan Yana aiki.
Matatar ta Dangote ta kara da cewa:
Harajin shigo da kaya na kaso 15 an tabbatar da shi ne tun 21 ga Oktoba bayan amincewar Shugaban Kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Matatar ta mayar da nauyin saukar farashin ga karancin bukata a kasuwannin duniya, da raguwa a farashin kayayyaki, da kuma karkatar kasuwannin man fetur.
Wani Labarin: Wike Ya kori Wasu Gwamnonin PDP guda uku daga Jam’iyar
Ta ce suna ci gaba da samar da mai mai inganci, da farashi mai gasa, tare da tabbatar da tsaro da dorewar samar da makamashi a Najeriya.
Matatar Dangote ta roki ‘yan Najeriya su yi taka-tsantsan da labaran da ba su da tushe, tare da neman kafafen yada labarai su rinka tabbatar da sahihin bayani kafin wallafawa.

