Wani bangare na jam’iyyar PDP dake samun goyon bayan ministan Abuja Nyesom Wike, da Sakataren jam’iyyar Sanata Samuel Anyanwu,ta kori gwamna Seyi Makinde na Oyo, da gwamna Bala Muhammad na Bauchi da Gwamna Dauda Lawal na Zamfara daga jam’iyyar.
Haka kuma bangaren na Wike ya kori tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyya na yankin Kudu, Chief Bode George, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar.
Bangaren ya kuma rushe shugabancin PDP na jihohin Bauchi, da Oyo,da Zamfara, da Yobe, da Lagos,da Edo da Ekiti, tare da bada umarnin kafa kwamitocin rikon kwarya domin gudanar da sabbin zaben shugabanni.
Daukar matakan sun biyo bayan rikicin da ya bulla sakamakon taron gangamin kasa na PDP da aka gudanar a Ibadan, wanda ya kai ga dakatar da Wike da magoya bayansa daga jam’iyyar a karshen mako.
A cikin sanarwar da Sakataren Jam’iyya, Sanata Sam Anyanwu, ya karanta, kwamatin zartaswa na PDP ya ce rahotannin da aka samu sun nuna sabon salo na siyasa da ya sabawa dokokin jam’iyya, da rashin bin hukuncin kotu, da aikata abubuwan da ke bata suna ga jam’iyyar.
TST Hausa ta rawaito cewa a ranar Asabar ne PDP ta zabi Sabbin Shigabanninta a Ibadan na jihar Oyo Inda a can kuma ta kori Wike saidai daga baya Shima a yanzu tsagin na Wike ya kori gwamnonin guda uku.
A taron na Asabar gwamnonin Adamawa da Plateau sun nuna kin amincewa da korar Wike

