Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL ya bada umarnin kara litar man fetur a sassa daban daban ciki harda Kano da Abuja da Lagos.
A yayinda yake aikewa da wani sakon murya daga kasa mai tsarki,ga Jaridar TST Hausa,daya daga cikin manyan dillalan man fetur daga kamfanin NNPC a Kano Injiniya Nuraddeen Aliyu yace an basu umarnin karin litar man fetur a gidajen mai na NNPCL mallakar gwamnatin tarayya.
Injiniya Nuraddeen Aliyu yace a Kano,zasu cigaba da sayar da litar man fetur daga naira 910 zuwa 955.
TST Hausa ta rawaito cewa a Abuja ana sayar da litar man fetur din akan naira 945 yayinda a Lagos yake kamawa naira 915 lita daya.
Injiniya Aliyu ya shaida cewa karin litar man yana da nasaba da yakin da akeyi tsakanin Kasar Iran da Isra’ila.
“Dole yakin da Iran takeyi da kasar Isra’ila ya shafi harkokin cinikayyar man fetur da sauran abubuwan bukatu a kasashen duniya,kancewar Iran na da karfin arzikin man fetur”-Inji Injiniya Aliyu.
Yayi fatan kawo karshen yakin akan lokaci domin samun sassauci.

