Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, ya ayyana matsalar rashin tsaro da fatara da yunwa a matsayin manyan abubuwan dake bukata kulawa ta gaggawa yana mai cewa dole ne a ɗauki matakai domin dakile su a faɗin Najeriya.
Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja yayin bikin Ranar Ma’aikata ta 2026, inda ya ce matsalolin tsaro da talauci sun zama manyan barazana ga zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin ƙasa.
Sakataren gwamnatin tarayya George Akume wanda ya wakilci shugaba Tinubu shine ya shaida hakan a bikin ranar Ma’ikata ta duniya da aka gudanar a wajen taro na Eagles Square dake Abuja.
A cewarsa, rashin tsaro na hana manoma noma yadda ya kamata, tare da kawo cikas ga harkokin kasuwanci da rayuwar yau da kullum, yayin da fatara ke ƙara tsananta wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
Shugaban ƙasa ya ce gwamnatinsa ta fara ɗaukar matakai daban-daban domin shawo kan matsalolin, ciki har da ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro, aiwatar da shirye-shiryen rage talauci, da kuma samar da damammakin ayyukan yi, musamman ga matasa.
Ya ƙara da cewa za a ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro da ƙungiyoyin ma’aikata domin tabbatar da samun nasara wajen magance matsalolin da suka addabi ƙasar nan.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu yankuna da kuma matsin tattalin arziki da ke shafar rayuwar jama’a.
A bangaren samar da aikinyi, sakataren gwamnatin ya ce akwai shirin na samar da damar aiki ga matasa 45,000 a Najeriya, inda aka tura su domin taimakawa wajen ƙarfafa tsaro da tabbatar da zaman lafiya a al’umma da yankunan ƙasar

