Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin sakin mutum 78 da jami’an tsaro suka kama bisa zargin hannu a harin da aka kai wa ayarin motocinsa a Abuja.
Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakinta, CSP Josephine Adeh, ta fitar ranar Litinin.
Ta ce an kama mutanen ne bayan wasu matasa sun yi luguden duwatsu da wasu abubuwa masu haɗari kan ayarin motocin shugaban ƙasar jim kaɗan bayan ya kammala sallar Juma’a a wani masallaci da ke Garki, Abuja, ranar 13 ga watan Nuwamba.
Rundunar ta bayyana cewa harin ya jawo lalacewar wasu motoci tare da jikkata jami’an tsaro.
Sai dai bayan shugaban ƙasar ya yi wa waɗanda ke da hannu a lamarin afuwa, fadar shugaban ƙasa ta umarci ’yan sanda da su yi wa waɗanda aka kama gargaɗi sannan su sake su.
’Yan sandan sun ce tuni aka fara gudanar da matakan da suka dace domin sakin mutanen.
Kwamishinan ’yan sandan Abuja, Ahmed Mohammed Sanusi, ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji tashin hankali da lalata dukiyoyin jama’a, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

