Wasu matasa sun kai hari kan ayarin motocin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ake zargin wasu ’yan daba ne suka kai a Karamar Hukumar Bichi ta Jihar Kano.
Lamarin ya faru ne a yammacin ranar Lahadi, 15 ga Nuwamba, 2026, lokacin da Kwankwaso da tawagarsa ke barin yankin bayan gudanar da rangadin siyasa a wasu kananan hukumomin jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa tawagar, wadda ta hada da dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar NDC, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, ta ziyarci kananan hukumomin Tofa, Rimin Gado, Kabo, Gwarzo, Shanono da Bagwai kafin isa Bichi.
Kakakin dan takarar gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tun kafin tawagar ta isa Bichi sun samu labarin cewa wasu mutane sun tare hanya domin hana su gudanar da taron siyasa
Ya bayyana cewa bayan sun isa garin, an fara jifar motocinsu da duwatsu, sannan wasu matasa dauke da makamai suka far musu bayan sun wuce sakatariyar karamar hukumar.
A cewarsa, harin ya jikkata wasu daga cikin magoya bayansu, yayin da aka lalata motoci da dama, inda ya ce da kansa ya ga motoci kusan bakwai da aka farfasa gilashinsu.
Sai dai kakakin ya bayyana cewa lamarin ba zai hana su ci gaba da gudanar da harkokin siyasarsu ba.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Jihar Kano ba ta fitar da sanarwar da ke tabbatar da cikakken bayani kan lamarin ba

