Attajirin ɗan kasuwar Najeriya, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana burinsa na ganin an samu ’yan Najeriya da suka fi shi kuɗi, yana mai cewa babban burinsa a yanzu shi ne ya kai matsayin attajirin Amurka, Elon Musk.
Dangote ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a matatar mansa da ke jihar Legas, inda ya nuna cewa har yanzu yana da burin faɗaɗa arzikinsa da kuma cimma manyan nasarorin kasuwanci.
Ya ce burinsa shi ne ya ga ’yan Najeriya sun ƙara samun wadata, tare da bayyana Elon Musk a matsayin wanda yake son kai matsayinsa ta fuskar arziki.
A cewar jerin attajiran duniya na mujallar Forbes na shekarar 2026, wanda aka tantance bisa darajar kadarori zuwa ranar 1 ga Maris, 2026, Elon Musk ne ya zo na farko a duniya da dukiyar da aka kiyasta ta kai dala biliyan 839.
A cewar mujallar Forbes ta shekarar 2026, dukiyar Alhaji Aliko Dangote ta kai kimanin dala biliyan 28.5 ($28.5 billion), kwatankwacin matsayinsa na attajirin da ya fi kowa arziki a Afirka.
Wannan na nufin dukiyar Elon Musk ta ninka ta Dangote kusan sau 29. Haka kuma, akwai tazarar kusan dala biliyan 810.5 a tsakaninsu.
Saidai kuma Dangote yace tun sama da shekara 45 bai taba tunanin cewa duk abinda yasa gaba baya yiyuwa ba.
“Har yanzu a ofishina na rubuta cewa Nothing is Impossible ” In Ji Dangote.

