Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da samun mutane 38 da suka kamu da wata cuta da har yanzu ba a gano nau’inta ba a wasu yankunan jihar.
Hukumar lafiya ta jihar ta ce mafi yawan waɗanda suka kamu da cutar suna ƙaramar hukumar Shinkafi, yayin da aka samu wasu a yankin Moriki da ke ƙaramar hukumar Zurmi.
Rahoton Cibiyar Kula da Ayyukan Gaggawa kan Lafiyar Jama’a ta jihar ya nuna cewa an tattara waɗannan alkaluma ne zuwa ranar 29 ga watan Oktoba na shekarar 2026.
Alamomin cutar sun haɗa da zazzaɓi, ciwon kai, rashin sha’awar cin abinci, amai, ciwon gaɓoɓin jiki da kuma raunin jiki.
Binciken farko ya nuna yiwuwar cutar zazzabin cizon sauro, ko kuma cututtukan da ke shafar ciki da hanji, ko sankarau ne ke haddasa matsalar, amma har yanzu ba a tabbatar da ainihin musabbabinta ba.
Gwamnatin jihar ta tura tawagar ƙwararrun ma’aikatan lafiya domin gudanar da bincike, duba marasa lafiya da kuma tattara samfuran jininsu domin gwaje-gwaje a ɗakin bincike da ke Sakkwato.
Kwamishiniyar Lafiya ta jihar, Dakta Nafisa Maradun, ta shawarci mazauna yankunan da abin ya shafa da su garzaya asibiti da zarar sun lura da alamomin cutar, tare da guje wa shan magani ba tare da shawarar likita ba.
Ta kuma buƙaci al’umma da su ba jami’an lafiya haɗin kai yayin da ake ci gaba da bincike domin gano musabbabin cutar da kuma dakile yaɗuwarta.

